…Yayin da aka dage alkalin wasan da ya ba Matic jan kati
Hukumar FA ta Ingila a shekaranjiya Laraba ne ta dage alkalan wasanni biyu da aka same su da yin laifi a wasanni daban-daban da suka yi wa alkalanci a karshen makon jiya. Na farko da aka dage shi ne Martin Atkinson, alkalin da ya hura wasan Chelsea da na Burnley, inda ya yi kuskuren ba […]
Hukumar FA ta Ingila a shekaranjiya Laraba ne ta dage alkalan wasanni biyu da aka same su da yin laifi a wasanni daban-daban da suka yi wa alkalanci a karshen makon jiya.
Na farko da aka dage shi ne Martin Atkinson, alkalin da ya hura wasan Chelsea da na Burnley, inda ya yi kuskuren ba Namanja Matic katin kora yayin da ya kyale dan kwallon Burnley Ashley Barnes wanda ya tunzura Matic har ya tunkude shi bayan ya yi masa mummunan keta.
Hukumar FA ta ce bai kamata alkalin wasa Atkinson ya bar dan kwallon Burnley Barnes ba duk da ketar da ya yi amma sai ya buge da ba Matic jan kati.
Sannan hukumar ta ce ta dage alkalin wasa Friend, wanda ya yi alkalanci a wasan da kulob din Southampton ya yi da na Liberpool a ranar Lahadin da ta wuce a gasar rukunin firimiya. Hukumar ta ce an dakatar da alkalin ne bayan an same shi da laifin kin bayar da bugun fanariti ga kungiyoyin biyu a lokuta da dama a lokacin da wasan ke gudana. Liberpool ce ta samu nasara a wasan da ci 2-0.