…Yayin da aka kashe wani dan kwallo a Rasha
An kashe dan kwallon kulob din Anzhi Makhachkala da ke Rasha mai suna Gasan Magomedeb a ranar Lahadin da ta wuce a hanyarsa ta komawa gida jim kadan bayan ya halarci atisaye. Al’amarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a lokacin da dan kwallon mai kimanin shekara 20 yake kan hyanyarsa ta komawa […]
An kashe dan kwallon kulob din Anzhi Makhachkala da ke Rasha mai suna Gasan Magomedeb a ranar Lahadin da ta wuce a hanyarsa ta komawa gida jim kadan bayan ya halarci atisaye.
Al’amarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Lahadi a lokacin da dan kwallon mai kimanin shekara 20 yake kan hyanyarsa ta komawa gida bayan ya halarci atisaye da kulob din nasa. An ce wadanda da ba a sansu ba ne suka bude wa motar matashin wuta kuma ya rasu ne a kan hanyar kai shi asibiti, kamar yadda bayanin da kulob din ya sanar a kafar sadarwarsa.
Kafar sardarwar wasanni ta Goal ta kalato cewa iyalan mamacin ne suka ji karar bindiga a bayna gidansu inda suka garzaya don ganin abin da ke faruwa sai suka tarar da dansu ne aka harba kuma suka yi yunkurin garzawa da shi asibiti, amma kafin su isa rai ya yi halinsa.
Kulob din ya ce ya zuwa hada wannan rahoto jami’an ’yan sandan yankin ba su gano wadanda suka aikata wannan kisan gilla ba amma dai har yanzu suna gudanar da bincike.
Wannan al’amari ya faru ne a yankin Dagastan da ke Rasha, yankin da ake danganta shi da yawan kai hare-hare i ga kungiyar Musulunci mai tsattausaran ra’ayi.
Da ma mafi yawan ’yan kwallo a Rasha ba kasafai suke ziyartar yankin Dagastan ba saboda yadda ake samun yawan samun tashe-tashen hankula.