…Yayin da Arsenal ta bayyana kungiyoyin da za su fafata a gasar cin kofin Emirates na bana
Kulob din Arsenal da ke Ingila ya bayyana kungiyoyin kwallon kafar da ya gayyato wadanda za su fafata a gsaar cin kofin kwallon kafa na Emirates a bana. kungiyoyin kwallon kafar da kulob din ya ce ya gayyato sun hada da na Lyon daga Faransa da billareal daga Sifen da kuma na Wolfsburg daga Jamus.Kulob […]
Kulob din Arsenal da ke Ingila ya bayyana kungiyoyin kwallon kafar da ya gayyato wadanda za su fafata a gsaar cin kofin kwallon kafa na Emirates a bana.
kungiyoyin kwallon kafar da kulob din ya ce ya gayyato sun hada da na Lyon daga Faransa da billareal daga Sifen da kuma na Wolfsburg daga Jamus.
Kulob din yana shirya gasar ce a duk shekara a shirye-shiryen tunkarar kakar wasa mai zuwa.
A ranar 25 ga watan Yuli ne kulob din Arsenal zai kece raini da na Lyon a gasar bayan kulob din billareal na Sifen da kuma na Wolfsburg daga Jamus sun fafata a wasan farko..
A ranar Lahadi 26 ga watan Yuli ne kulob din Arsenal zai buga wasan karshe da na Wolfsburg bayan Lyon ta hadu da na billareal.
Ana ba da maki uku ne ga duk kulob din da ya samu nasara a gasar yayin da ake ba da maki daya a kunnen doki. Sannan ana bada maki ga kowace kwallon da aka zura a raga, saboda haka duk kulob din da ya fi yawan maki da kuma yawan zura kwallaye a raga a gasar ce yake zama zakara.
Tun a shekarar 2007 ne kamfanin Emirates da ya mallaki jiragen sama yake daukar nauyin gasar wanda kulob din Arsenal na Ingila ke shiryawa.