… Yayin da bictor Moses zai koma Eberton
Shahararren dan kwallon gaba a kulob din Chelsea da ke Ingila kuma dan kwallon Najeriya Super Eagles, bictor Moses a karshen makon nan ake sa ran zai canza sheka zuwa kulob din Eberton da ke Ingila.Rahoton da kafar sadarwar Daily Mail ta fitar ya nuna kulob din Eberton zai sayi Moses ne a kan Fam […]

Shahararren dan kwallon gaba a kulob din Chelsea da ke Ingila kuma dan kwallon Najeriya Super Eagles, bictor Moses a karshen makon nan ake sa ran zai canza sheka zuwa kulob din Eberton da ke Ingila.
Rahoton da kafar sadarwar Daily Mail ta fitar ya nuna kulob din Eberton zai sayi Moses ne a kan Fam miliyan 8 kuma tuni dan kwallon da kulob din Chelsea suka amince da batun canza shekar tasa.
Shi dai sabon Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya nuna bictor Moses yana daga cikin ’yan kwallon da ba zai yi amfani da su a kakar wasa ta bana ba, hasalima biyar daga cikin tsofaffin ’yan wasan ne kadai zai yi amfani da su, sauran kuwa ciki har da Moses sai dai su canza sheka.
Moses ya taba yin kwallo a karkashin sabon Kocin Eberton Roberto Martinez a lokacin da yake horarwa a kulob din Wigan.