…Yayin da Carlos Tebez ya koma Jubentus
Shahararren dan kwallon Manchester City da ke Ingila Carlos Tebez ya koma kulob din Jubentus da ke Italiya a kan Fam miliyan 10.Kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, dan kwallon zai rika karbar albasbhin Fam miliyan 4 da dubu 600 a shekara.Tebez, dan kimanin shekara 29, ya koma kulob din City da ke Ingila […]

Shahararren dan kwallon Manchester City da ke Ingila Carlos Tebez ya koma kulob din Jubentus da ke Italiya a kan Fam miliyan 10.
Kamar yadda kafofin watsa labarai suka ruwaito, dan kwallon zai rika karbar albasbhin Fam miliyan 4 da dubu 600 a shekara.
Tebez, dan kimanin shekara 29, ya koma kulob din City da ke Ingila ne daga kulob din Manchester United.
A shekaru biyun da suka wuce ya yi ta samun sabani a tsakaninsa da tsohon kocin kulob din City Roberto Mancini inda ya yi ta kokarin canza sheka amma abin ya ci tura sai a wannan lokaci da shi ma koci Mancini ya bar kulob din bayan an sallame shi.
Kulob din bai gabatar da Tebez ga ’yan jarida ba a shekaranjiya Laraba saboda wadansu batu da ba su gama tattaunawa da dan kwallon ba. Amma rahotanni sun tabbatar yarjejeniya a tsakanin kulob din da shi ta kai matsayin kashi 90 daga cikin 100 don haka ana sa ran nan da ’yan kwanaki komai zai daidaita.