…Yayin da Jamus ta fitar da Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya na maza
A jiya Alhamis ne kasar Jamus ta fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da yanzu haka yake gudana a kasar Newzealand. Wasan, wanda ya gudana da misalin karfe 8 da rabi na safe agogon Najeriya, tun a minti na 19 da fara wasa ne dan kwallon […]
A jiya Alhamis ne kasar Jamus ta fitar da Najeriya a gasar cin kofin duniya na ’yan kasa da shekara 20 (U-20) da yanzu haka yake gudana a kasar Newzealand.
Wasan, wanda ya gudana da misalin karfe 8 da rabi na safe agogon Najeriya, tun a minti na 19 da fara wasa ne dan kwallon Jamus mai suna Lebin Oztunali ya zura kwallo a ragar Najeriya amma duk yunkurin da Najeriya ta yi don ta fanshe hakan bai yiwu ba. Haka aka tashi wasan da ci 1-0.
Yanzu an fitar da Najeriya daga gasar kenan, sannan Jamus kuma za ta hadu da kasar Mali a wasan kusa da na karshe watau Kwata-Fainal a jibi Lahadi idan Allah Ya kaimu.
kasashen Mali da Senegal ne suka haye matakin kwata-fainal daga Afirka yayin da aka fitar da Najeriya da kuma Ghana daga gasar.