…Yayin da Yaya Toured ya sake lashe Gwarzon dan kwallon Afirka a karo na hudu
Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kuma dan asalin Ibory Cost Yaya Toure ya sake lashe Gwarzon dan kwallon Afirka a karo na hudu a gagarumin bikin da aka gudanar a Jihar Legas a makon da ya gabata. Yaya Toure dan kimanin shekaru 31 a duniya ya zama Gwarzon dan kwallon kafa […]
Fitaccen dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City kuma dan asalin Ibory Cost Yaya Toure ya sake lashe Gwarzon dan kwallon Afirka a karo na hudu a gagarumin bikin da aka gudanar a Jihar Legas a makon da ya gabata.
Yaya Toure dan kimanin shekaru 31 a duniya ya zama Gwarzon dan kwallon kafa na farko da ya lashe gasar har sau hudu a jere.
Ya kasa abokan hamaiyyarsa da suka hada da mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagle bincent Enyeama wanda yake yi wa kungiyar kwallon kafa ta Lille da ke Faransa wasa da dan kasar Gabon wanda ke bugawa kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund mai suna Pierre-Emerick Aubameyang.
dan wasa Toure ya yi kan-kan-kan da fittacen dan wasan kulab din Eberton na Ingila dan kasar Kamaru, Samuel Eto wanda shi ma ya taba lashe gasar har sau hudu amma ba a jere ba, amma shi Yaya Toure ya lashe sau hudu a jere ne.
Dalilin da ya sa Yaya Toure ya zarta Eto shi ne saboda ya lashe gasar a shekarar 2011 da shekarar 2012 da shekarar 2013 da kuma shekarar 2014 a jere.
Masu horor da ’yan wasa da daraktoci na kasashen 54 sun sake zabar Yaya Toure ne saboda gwanintar da ya rika nunawa a ciki da wajen kasarsa.
Gwanintarsa ta hada da kai kulab din Manchester City na Ingila lashe gasar rukunin firimiya a bara da taimakawa Kwaddebuwa hayewa gasar cin kofin duniya da aka yi a Brazil a shekarar 2014.
To sai dai kuma an zabi Ndombe Mubale ’yar kasar Congo wacce ta ci kwallo shida a gasar kalubalen kwallon kafa ta mata a matsayin wacce ta fi taka leda a Afirka.