Yemi Mobolade: Dan Najeriya ya zama Magajin Gari a Amurka

Mobolade wanda dan gudun hijira ne daga Najeriya hamshakin dan kasuwa ne.

Yemi Mobolade: Dan Najeriya ya zama Magajin Gari a Amurka

Wani haifaffen Najeriya, Yemi Mobolade ya yi nasarar lashe zaben kujerar Magajin Gari a Colorado Springs da ke Jihar Colorado a Amurka.

Mobolade ya kasance bakar fata na farko da zai dare mukamin a Colorado Springs, birni na biyu mafi girma a Jihar Colorado ta Amurka da ke da tarihin kasancewa tungar masu ra’ayin mazan jiya.

Bayanai na cewa, Mobolade dan gudun hijira ne daga Najeriya, kuma hamshakin dan kasuwa ne da bai taba rike wani zababben mukami a baya ba.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa shi ne koma bayan siyasa na baya-bayan nan ga jam’iyyar Republican a jihar da ta kasance jiha mai fada a ji.

Mobolade da iyalansa.

Mobolade, wanda ya sami amincewar wasu fitattun ’yan jam’iyyar Republican, ya mayar da hankali kan batutuwa kamar daukar karin jami’an ’yan sanda, samar da gidaje masu saukin kudi, adana ruwa da magance matsalolin samun ayyukan kasuwanci.

Mobolade, mahaifin yara kanana uku wanda da ke auren wata ma’aikaciyar jinya, ya yi kaura daga Najeriya zuwa birnin da ke da yawan jama’a kusan 485,000 da aka sani da sansanonin soji da kuma kasancewa cibiyar Kiristanci na Ikklesiyoyin bishara inda ya fara kafa majami’a tsawon fiye da shekaru goma da suka wuce, kuma ya bude gidan sayar da abinci.

Ya kuma yi aiki a cikin gwamnatin birni a bangaren inganta ci gaban tattalin arziki da kuma taimaka wa masu kananan sana’o’i.

Shi ne zai kasance Magajin Gari na farko wanda ba dan jam’iyyar Republican tun bayan da birnin ya fara zaben kantomomi shekaru 45 da suka gabata, a cewar Jaridar The Gazette.

AP