Yerima Ibn Mahmud ya zama sabon Sarkin Ngazargamu
Ibn Mahmud ya kasance Turakin Ngazargamu na tsawon shekaru 16 kuma tsohon Kwamishina da tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Yobe
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗin Alhaji Yerima Ibn Mahmud a matsayin sabon Sarkin Ngazargamu.
An sanar da naɗin ne a cikin wata sanarwa da Muƙaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, Dakta Mohammed Goje, ya fitar a ranar Juma’a.
Ibn Mahmud zai gaji marigayi Sarkin Ngazargamu, Alhaji Tijjani Ibn Saleh Geidam, wanda ya rasu a ranar Talata a ƙasar Masar bayan fama da doguwar rashin lafiya. An yi jana’izarsa a ranar Juma’a a Damaturu.
Kafin wannan naɗi, Ibn Mahmud ya riƙe muƙamin Kwamishinan Bunƙasa Kiwo na Jihar Yobe. Haka kuma, ya kasance Turakin Ngazargamu na tsawon shekaru 16.
- DSS ta kama matashi kan zargin safarar makamai a Kano
- Bayan yunƙurin sasanci da ’yan bindiga sun kai hari a Katsina
Sabon sarkin ya taɓa riƙe muƙamai daban-daban a gwamnati, ciki har da zama ɗan Majalisar Dokokin Jihar Yobe da kuma kwamishina a jihar a lokuta mabambanta tsakanin shekarar 2007 da 2026.
A cewar sanarwar, ya bayar da gagarumar gudummawa wajen tafiyar da gwamnati, tsara manufofi da kuma bunƙasa tattalin arziki da zamantakewa a tsawon shekarun da ya yi yana hidimar jama’a.
Yayin da yake taya sabon sarkin da al’ummar masarautar murna, Gwamna Buni ya buƙace shi da ya yi amfani da ƙwarewarsa wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba.
Ya ce, “Ina taya sabon Sarkin Ngazargamu da ɗaukacin al’ummar masarautar murnar wannan naɗi.
“Ina kira ga Mai Martaba da ya yi amfani da gogewarsa wajen haɗa kan jama’a, inganta zaman lafiya da zaman tare cikin aminci, tare da ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki a masarautar, Jihar Yobe da Nijeriya baki ɗaya.”
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar masarautar da su bai wa sabon sarkin cikakken goyon baya domin samun nasarar gudanar da ayyukansa.
Ya ce, “Ina kira ga al’ummar masarautar da su bai wa sabon Sarkin cikakken goyon baya domin ya sauke nauyin da ke kansa cikin jajircewa, nagarta da inganci, domin amfanin jama’a da kuma ci gaba da wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da wadata a masarautar.”
Gwamna Buni ya yi addu’ar Allah Ya ba sabon Sarkin hikima, lafiya da kuma mulki mai cike da zaman lafiya da albarka.