Yerima Ngama ne ya jefa PDP cikin rikici a Jihar Yobe – Ngordi
Jam’iyyar PDP mai adawa a Jihar Yobe na fuskanta rikice-rikice cikin gida, inda hakan ya haifar da baraka a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar har ya kai ga darewarta zuwa bangarori biyu; wato bangaren tsohon Ministan Harkokin ’Yan sanda Alhaji Adamu Maina waziri wanda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar har karo uku ba […]
Jam’iyyar PDP mai adawa a Jihar Yobe na fuskanta rikice-rikice cikin gida, inda hakan ya haifar da baraka a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar har ya kai ga darewarta zuwa bangarori biyu; wato bangaren tsohon Ministan Harkokin ’Yan sanda Alhaji Adamu Maina waziri wanda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar har karo uku ba tare da nasara ba, da kuma bangaren tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi Alhaji Yerima Ngama. Wani dattijo a Jam’iyyar PDP a jihar Alhaji Muhammad Ngordi ya yi fashin baki kan makasudin rikicin da halin da ake ciki a yanzu:
Aminiya: A matsayinka na dattijo a Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe me ya haddasa rikicin da jam’iyyar ke fuskanta har ya kai ga darewarta gida biyu duk da ba ita ke da rike da madafun iko a jihar ba?
Ngordi: Da farko dai musabbabin rashin fahimtar da ta taso tsakanin wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar har ta haddasa darewarta gida biyu shi ne, matsaloli ne da suka taso tsakanin tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi Alhaji Yerima Ngama lokacin da yake Minista daga Jihar Yobe, kasancewarsa minista a lokacin shi ne jagoran Jam’iyyar PDP a jihar saboda ba ta da Gwamn. To shi ne sai ya nemi a ba shi matsayin shugaban jam’iyyar a shiyyar da ya fito ta Arewacin jihar Yobe. Mu kuma a matsayinmu na dattawa sai muka zauna muka sahale masa, sai a ka yi rashin sa’a a lokacin maimakon Ministan ya kira taron zaben sababbin shugabanninta a Damaturu fadar jiha kamar yadda yake bisa ka’ida sai kawai ya yi gaban kansa ya kira taron a Jakusko hedikwatar karamar Hukumar Jakusko duk da cewa mun neme ya dakatar da zaben saboda halin da jihar ke ciki na rikice-rikice amma ya kekasa kasa ya ki ya gudanar da taronsa gaba gadi.
To bayan da suka yi zaben, nan da nan sai Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta ce ba ta amince da zaben shugabannin PDP da aka yi a Jihar Yobe ba, domin ba a yi shi bisa ka’ida ba, sai hukumar ta rubuta wa uwar jam’iyya ta kasa kan wannan lamari har sau bakwai amma kuma a lokacin aka yi rashin sa’a tsohon shugaban jam’iyyar ta kasa Dokta Bamanga Tukur ya sa kafa ya shure batun ya ki daukar mataki a kai.
To sai mutane irin su Alhaji Adamu Maina Waziri da Alhaji Abba Gana Tata da sauransu suka ce, lallai zama bai same su ba dole ne a yi wa tufkar hanci, shi ne suka tashi tsaye suka ce ya kamata wannan abu a gyara shi. Kuma ana cikin haka sai Hukumar INEC ta sake rubuto takarda ta tura ga uwar jam’iyyar ta sanar da ita cewa, muddin aka ce za a tura ’yan takarar jam’iyyar a karkashin wancan shugabanci da ta ce ba ta yarda da shi ba, to, ba za ta amince da su ba.
Aminiya: karkashin wane shugabanci ke nan?
Ngordi: karkashin shugabancin Alhaji Lawan Gana da tsohon Minista Yerima Ngama ke mara wa baya. To a halin da mu kuma muke hangen lallai akwai yiwuwar a wannan karon za mu karbe mulkin jihar daga hannun gwamnatin APC a 2015, sai muka ga ya kamata mu tashi haikan don gyara, saboda kada a yi mana sakiyar da ba ruwa, sai kuma muka yi sa’ar sabon shugaban jam’iyya a matsayinsa na wanda ya ce zai yi adalci ga kowa da ya ga haka sai nan da nan ya ce ya rusa shugabancin jam’iyyar a jihar tare da nada kantoman tunda da ma ya ce duk jihar da ke da matsala makamancin irin ta Jihar Yobe zai bi da su daidai da kuma umartar bangarorin su ba da mutum bibbiyu don tafiya da su wadanda za su gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar da ’yan jam’iyya za su amince da su. Abin mamaki jin wannan hukunci da uwar jam’iyya ta yi sai bangaren Yerima Ngama suka ce atafau ba su amince da rusa shugabannin jam’iyyar ba, suka nufi kotu alhali harkoki irin na rikicin jam’iyya ba a zuwa kotu tunda akwai iyayen jam’iyya domin kai jam’iyya kotu tamkar bijire wa dokar jam’iyya ce. Duk da cewa na ji an ce wai sun ba da wakilansu biyu kamar yadda uwar jam’iyyar ta ce a yi.
Aminiya: To ina matsayinku a yanzu?
Ngordi: To matsayinmu a Jam’iyyar PDP a jihar dai yanzu mun amince da za a yi zaben sababbin shugabannin jam’iyyar da ’yan jam’iyyar ke so, tunda an ma fara sayar da fom na shiga takarar, kuma nan gaba kadan za a yi zaben mazabu daga nan sai kananan hukumomi har a kai ga matakin jiha a watan Nuwamban da ke tafe in Allah Ya so.
Aminiya: Kana ga ba ku makara ba game da yunkurin naku kasancewar lokacin zabe ya karato?
Ngordi: A ganina da kuma matakin jam’iyyarmu ta PDP ba mu makara ba, domin kuwa ai da sauran lokaci ballantana ma uwar jam’iyya ta san da halin da muke ciki.
Aminiya: A matsayinka na dattijo a Jam’iyyar PDP a Jihar Yobe wane kira za ka yi ga bangaren Ngama don ku gudu tare ku tsira tare, hakarku ta cimma ruwa na kwace jihar daga APC?
Ngordi: To, lallai da yake tsohon Minista Ngama dan takara ne, to mai kaza a lajihu ba ya jimirin as! Don haka akwai bukatar ya zo a hada kai don a kai jam’iyyar ga nasara. In mutum ya san na da mutane, ai ba zai ji tsoron komai ba, ya zo a yi gwagwarmayar da shi. In koyon siyasa yake yi, to ya zo ya koya cikin jama’a in kuma ya iya, to ya zo ya nuna wa mutane ya iya. Don haka jam’iyya ke gaba da kowa ya zo a sa ta gaba don kaiwa ga nasara. Ina ba shi shawara ya canja halin da ya dauka, ya zo a hada kai muddin da gaske yake yi yana son ci gaban Jam’iyyar PDP don a gudu tare a tsira tare a kuma rufa baya ga duk wanda Allah Ya bai wa mulki.
Aminiya: Me za ka ce dangane da yadda gwamnatin Jihar Yobe ke gudanar da mulki?
Ngordi: To mu dai a Jam’iyyar PDP ba mu fatan koda za mu mulki jihar mu yi kwatankwacin rashin adalcin da shugabannin jihar ke gudanarwa a karkashin Jam’iyyar APC. Da farko babu wani aiki a kasa da za a ce an yi wa al’umma, ga bakin talauci da ke addabar al’ummar jihar, ga uwa uba shugabannin jihar ba sa ma zama a jihar ballantana su san damuwar jama’a. Kullum suna yawace-yawace ba tare da an kula da rayuwar al’umma ba.