Yi wa jama’a hidima nake so ba mulki ba – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Honourabul Yakubu Dogara ya ce ya sadaukar da dukan nasarorin da ya samu ga al’ummar mazabarsa domin amincewar da suka nuna masa ne kashin bayan samun wannan nasara. Da yake jawabi a wajen taron karramawar da al’ummar mazabarsa suka shirya masa don bikin cikarsa shekara 50 a ranar Asabar da ta gabata […]

Yi wa jama’a hidima nake so ba mulki ba – Dogara

Shugaban Majalisar Wakilai Honourabul Yakubu Dogara ya ce ya sadaukar da dukan nasarorin da ya samu ga al’ummar mazabarsa domin amincewar da suka nuna masa ne kashin bayan samun wannan nasara.

Da yake jawabi a wajen taron karramawar da al’ummar mazabarsa suka shirya masa don bikin cikarsa shekara 50 a ranar Asabar da ta gabata a garin bogoro da ke Jihar Bauchi, Barista Yakubu Dogara ya ce, mutanen bogoro da Dass da Tafawa balewa ne suka share hanyar zamansa Shugaban Majalisar Wakilai saboda sake zabensa duk da kalubale da adawar da ya fuskanta, kuma wannan ne ya kai shi matsayin da zai iya yin tasiri wajen kawo musu ayyukan ci gaba da za su amfani mazabar da Jihar Bauchi da kuma yankin Arewa maso Gabas.

Shugaban Majalisar wanda ya yi godiya ga Allah kan yadda Ya ba shi damar cimma dimbin nasarorin da ya samu, ya ce ya fi damuwa ya samu damar yi wa jama’a hidima maimakon samun mukamin mulki. “Ba ni sha’awar mukami, ina sha’awar yi wa jama’a hidima ce. Mukami ba ya da wani amfani a wurina, abin da na fi so shi ne in yi wa jama’a hidima. Idan na kammala aikina na dan majalisa Ubangiji zai gusa da ni zuwa wani matsayi da zan kara yin hidima ga jama’ata. Ba domin taimakon Allah ba, ba zai yiwu in samu wadannan abubuwa ba, kuma wannan ne ya sa muke nan domin yin godiya ga Allah kan yin amfani da ni hakan ya samu, ba wai don murnar haihuwata ba, a’a don mu yi godiya ga Allah,” inji shi.

Ya ce “Ba domin zuba jarinku ba, babu ta yadda za a yi ku tuka mota daga nan zuwa Bauchi tafiyar kilomita 82 ba tare da haduwa da rami daya a kan gangariya kwaltar ba. A lokacin ma ban zama Shugaban Majalisar Wakilai ba. Wannan aiki ya wuce aikin dan majalisa Allah ne Ya sa hakan ta auku. Saboda amanar da kuka ba ni a yau muke da Shugaban Majalisar Wakilai, wannan abin alfahari ne a gare mu. Saboda tsayuwarku muka samu wanda ya yi kusa da inda Tafawa balewa ya kai. Ina farin ciki Allah Ya saka masa kan sadaukarwa da ya yi.”

Ya kara da cewa: “Kuma sakamakon jarin da kuka zuba ne a yau muka samu Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC). Ba domin ina Shugaban Majalisar Wakilai, hakan zai yi wuya ya samu. Duk lokacin da kuka Hukumar NEDC, to ku sani sadaukar da kan mutanen wannan mazaba ce da na Jihar Bauchi suka kawo ta.”

“Kuma saboda jarin da kuka zuba ne muka tara sama da Naira miliyan 300 domin tallafa wa ’yan gudun hijirar yankin Arewa maso Gabas da sauran yankunan Najeriya. Babu wanda zai taba ko kwabo daga wannan kudi,” inji shi.

Shugaban ya ce barnar da ta’addancin Boko Haram ya haifar a ’yan shekarun da suka gabata za a dauki fiye da shekara 20 ba a magance ta ba.