Yin addu’a ba fasawa (1)
Ku rika yin addu’a ba fāsawa (1 Tasalonikawa 5:17)A wannan makon da yardar Ubangiji za mu yi bincike ne a kan yin addu’a ba fasawa.A zamanin da muke ciki yau, addu’a aba ce mafi muhimmanci ga rayuwarmu a koyaushe. Addu’a hanya ce ta sadarwa tsakaninmu da Ubangijinmu. Mukan nuna shaidar godiyarmu a gare Shi ta […]
Ku rika yin addu’a ba fāsawa (1 Tasalonikawa 5:17)
A wannan makon da yardar Ubangiji za mu yi bincike ne a kan yin addu’a ba fasawa.
A zamanin da muke ciki yau, addu’a aba ce mafi muhimmanci ga rayuwarmu a koyaushe. Addu’a hanya ce ta sadarwa tsakaninmu da Ubangijinmu. Mukan nuna shaidar godiyarmu a gare Shi ta wurin yin addu’a, haka nan mukan yabe Shi mu kuma nemi taimako daga wuriSa, shi ya sa a yau idan ba ka iya yin addu’a ba, lallai kana cikin babbar damuwa. Mutane da dama sun fi son wadansu su yi musu addu’a (sun dauki addu’a aba ce da za ka saya da kudi – don sukan ba da kudi ko kyauta don wani ya yi musu addu’a), alhali kuwa Ubangiji Allah Ya ba mu ’yancin yin addu’a kai-tsaye. Idan har ba ka yarda da haka ba, kana biyan wani ne ya yi maka shaidar godiya idan Ubangiji Allah Ya yi maka wani babban abin alheri? Ko kuma idan kana cikin tsakiyar halin hadari ko mutuwa kana iya biyan wani ya yi maka addu’a ne don fita daga wannan hali? Abin tausayi za ka ga wasu sun fi yarda cewa sai sun samu wani ko idan sun ba da kudi ga wani kafin Ubangiji Ya amshi addu’arsu, mu yi hankali da malamai da annabawan karya kamar yadda Ubangiji Ya umarce mu a cikin maganarSa; Matiyu 7:15 “Ku kula da annabawan karya, wadanda sukan zo muku da siffar tumaki, amma a zuci kyarketai ne masu kawa. Za ku gane su ta irin aikinsu. A iya ciran inabi a jikin kaya, ko kuwa baure a jikin sarkakkiya? Haka kowane itacen kirki yakan haifi kyawawan ’ya’ya. Mummunan itace kuwa yakan haifi munanan ’ya’ya. Kyakkyawan itace ba dama ya haifi munanan ’ya’ya. Haka kuma mummunan itace ba dama ya haifi kyawawan ’ya’ya. Duk itacen da ba ya ’ya’ya masu kyau, sai a sare shi a jefa a wuta. Don haka, da irin aikinsu za a gane su.”
Hada kai tare don yin addu’a ba laifi ba ne domin almajiran Yesu Almasihu bayan tashinsa daga mattatu sun hada kansu wuri daya kuma sukan yi addu’a tare amma ba wai Bitrus ko Manzo Bulus ne yake yin addu’a a madadinsu ba, suna da shugaba ne don jagora da karfafawa kuma kwaba ga wadanda sun bai wa Shaidan zarafi. Hakan nan yin addu’a a madadin wani ko wasu ko shugaba ne ko kasa a zamanka na Kirista (ba tare da sai ka ba da ko an ba ka kudi ko wasu kyaututtuka ba) abu ne mai kyau mai albarka kuma a gaban Ubangiji. 1 Timoty 2:1-2 Da farko dai ina gargadi, cewa a yi ta rokon Allah, ana addu’a, ana godo, ana gode wa Allah saboda dukkan mutane, da sarakuna da kuma duk wadanda suke a manyan makamai, don mu zauna lafiya, rai a kwance, muna bin Allah sosai a cikin natsuwa.” Shi ya sa Ubangiji Ya umurce mu da mu zama masu yin addu’a a koyaushe, yin haka kan karfafa rayuwarmu, lafiyarmu ta jiki da ta ruhaniya da kuma zumunci da juna a nan duniya.
Kowace rana na dauke da albarka da matsalolint, ta wurin yin addu’a mukan nuna godiyarmu ga Ubangiji a kowace rana cikin kowace hali 1Tasalonikawa 5:17-18 “Ku rika yin addu’a ba fasawa. Kuna godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.” Mukan kuma nemi nufin Ubangiji don jagora da kuma kariya da nasara a kan kowace irin jarabawa.
Babu wata hujja cewa ba zan iya addu’a ba don wai ba ka iya ba ko aiki ko rashin lokaci, ai lokaci shi ne zama cikin rayayyu a kowace rana, da iyawar kanmu ne muke rayuwa? Idan ba haka ba, me zai hana ka ko ki shaidar godiya ga Allah cewa Ya bar ka cikin rayayyu har zuwa wannan rana, kuma me zai hana mu neman jagorarSa cikin wannan rana don ba mu san abin da zai faru ba a gaba. Ashe akwai dalilai da dama da suka kamata mu zama masu yin addu’a a koyaushe. Kullum muna ta guna-guni cewa muna shan wahala, Ka yi ko kin yi addu’a a kan wannan batu yau? Matiyu 7:7-11 “Ku yi ta roko, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta kwankwasawa, za a kuwa bude muku.” (Amma fa rokon bisa nufinSa da kuma ban-gaskiya – 1Yahaya 5:14 “Wannan ita ce amincewarmu a gabansa, wato, in mun roki komai bisa ga nufinsa, sai ya saurare mu.” Matiyu 21:22 “Komai kuka roka da addu’a, in dai kuna da ban-gaskiya, za ku samu.” Wani lokaci mukan yi roko amma kuma ba ma samu ko kuwa yakan dauki lokaci mai tsawo kafin mu samu biyan bukata, dalili kuwa shi ne: Yakubu 4:3 “Kukan yi addu’a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku batar a kan nishadinku.” Sai mu lura a duk lokacin da za mu yi addu’a mu nemi nufin Allah ya kasance cikin rayuwarmu amma ba namu nufi ba.
Akwai misalai da dama da za mu iya yin koyi da su domin gina rayuwarmu ta wurin yin addu’a: Annadi Musa ya nemi tagomashi a wurin Ubangiji Allah (Fitowa 33:13-14)
“Yanzu ina rokonKa idan na samu tagomashi a gare Ka, Ka nuna mini hanyoyinKa domin in san Ka, in kuma samu tagomashi a wurinKa, Ka kuma tuna, wannan al’umma jama’arKa ce.” Ubangiji kuwa Ya ce, “Zan tafi tare da kai, zan kuma hutashe ka.”
Sarki Dauda ya nemi jinkan Ubangiji (Zabura 51:1-8) “Ka yi mini jinkai, ya Allah, saboda madawwamiyar kaunarka. Ka shafe zunubaina, saboda jinkanka mai girma! Ka wanke muguntata sarai, Ka tsarkake ni daga zunubina! Na gane laifina, Kullum ina sane da zunubina. Na yi maKa zunubi, Kai kadai na yi wa, na kuwa aikata mugunta a gare Ka…”
Manzo Bulus ya yi wa masu bi addu’a (Filibiyawa 1:9-11) “Addu’ata ita ce, kaunarku ta rika habaka da sani da matukar ganewa, domin ku zabi abubuwa mafifita, ku zama sahihai, marasa abin zargi, har ya zuwa ranar Almasihu, kuna da cikakken sakamakon aikin adalci da yake samuwa ta wurin Yesu Almasihu, wannan kuwa duk domin daukakar Allah ne da yabonSa.”
Annabi Yunusa ya yi addu’a ta Godiya ga Allah (Yunusa 2:1-10) “Sai Yunusa ya yi addu’a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin, ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka kuwa amsa mini…”
Yesu ya koya wa almajiransa yadda za su yi addu’a (Matiyu 6:9-13) “Saboda haka sai ku yi addu’a kamar haka, ‘Ya Ubanmu, Wanda Yake cikin Sama, A kiyaye sunanka da tsarki. MulkinKa ya zo, A aikata nufinKa a duniya kamar yadda ake yi a sama. Ka ba mu abincinmu na yau. Ka gafarta mana laifuffukanmu, Kamar yadda mu ma muke gafarta wa wadanda suke yi mana laifi. Kada Ka kai mu wurin jarabawa, amma ka cece mu daga mugun.’ Domin in kun yafe wa mutane laifuffukansu, Ubanku na sama zai yafe muku. In kuwa ba ku yafe wa mutane laifuffukansu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”
Ubangiji Allah Yana bukatar mu zama masu kira bisa sunanSa ta wurin addu’o’in godiya, yabo da daukaka sannan neman taimakonSa, domin Ya alkawarta mana cewa idan muka roka Shi zai ba mu. Shi ya sa yin addu’a na da muhimmanci kwarai da gaske cikin rayuwar mai bin Yesu Almasihu don samun ginuwa cikin rayuwarmu ta ruhaniya da ta jiki kuma.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa idan Ubangiji Allah Ya bar mu cikin masu rai.
Shallom.