Yin addu’a ba fasawa (2)

Ku rika yin addu’a ba fasawa (1 Tasalonikawa 5:17)Muna yi waUbangiji Allah godiya da Ya bar mu cikin rayayyu a wannan makon. Barkanmu kuma da sake saduwa inda za mu ci gaba cikin bincikenmu kan yin addu’a ba fasawa. Afisawa 6:18. A koyaushe kuna addu’a da roko ta wurin ikon Ruhuba fasawa. A kan wannan […]

Yin addu’a ba fasawa (2)
Yin addu’a ba fasawa (2)

Ku rika yin addu’a ba fasawa (1 Tasalonikawa 5:17)
Muna yi waUbangiji Allah godiya da Ya bar mu cikin rayayyu a wannan makon. Barkanmu kuma da sake saduwa inda za mu ci gaba cikin bincikenmu kan yin addu’a ba fasawa.
Afisawa 6:18. A koyaushe kuna addu’a da roko ta wurin ikon Ruhuba fasawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matukar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu’a.
Idan mun kula za mu ga cewa mutane da dama yanzu ba sa addu’a sai dai idan sun shiga wata damuwa ko suna bukatar wani abu. Littafi Mai tsarki na cewa mu rika yin addu’a ba fasawa; ko cikin dadi ko cikin wahala. Ai ba ma zuwa ganin iyayenmu don mun shiga wata matsala ko kuma muna neman biyan bukata, amma don mu sada zumunci mu kuma ba su darajarsu ta iyaye har ma su ba mu shawarwari masu muhimmanci da za su karfafa mu su kuma taimake mu. Hakan nan addu’a take, sada zumunci da Ubangiji da kuma ba Shi girmanSa da darajarSa. Wasu lokutan mukan bar matsalolin da muke ciki su hana mu yin addu’a, alhali kuwa a lokacin ne ya kamata mu yi addua’a da naciya. Ubangiji Yakan bar wasu jarabawa da dama don mu girma cikin saninSa, domin a duk lokucin da muka shiga damuwa Ubangiji Allah Yana so Ya ga ko za mu kira bisa sunanSa ko ba za mu yi ba shi ya sa Ya ce mu rika yin addu’a ba fasawa. Sai mu sani cewa ba ma rayuwar nan da ikon kanmu, ba za mu iya yin komai ba in ba tare da yardarSa ba, saboda haka kada mu bar matsalolin da muke fuskanta su raba mu da Ubangiji da kuma sanin karfin ikonSa, domin Yana da ikon ceto mu daga cikin kowane irin yanayi da muka samu kanmu a ciki. Filibiyawa 4:6-7 “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roko, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu. Mu sanar da Shi, Ubangiji Shi ne maganin komai, kada mu karaya idan har ba mu samu biyan bukatunmu a lokacin da muke zato ba, gama hanyarSa da tamu ba daya suke ba hakan nan shirinSa da namu sun bambamta. Irimiya 29:11-13: “Gama Na san irin shirin da Na yi muku, Ni Ubangiji Na fada. Shiri na lheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya. Sa’annan za ku yi kira a gare Ni, ku yi addu’a a wuriNa, Zan kuwa ji ku. Za ku neme Ni ku same Ni, idan kun neme Ni da zuciya daya. ”Ishaya 55:8-9 Ubangiji Ya ce, “TunaniNa ba kamar irin naku ba ne, al’amuraNa kuma daban suke da naku. Kamar yadda sammai suke can nesa da kasa, haka al’amuraNa da tunaniNa suke nesa da naku. Shi ya sa za ka ga wasu sun fada tarkon Ibilis don neman biyan bukatunsu a daidai wannan lokacin da suke bukata misali, haihuwa, neman dukiya, neman matsayi a wurin aiki, nasara cikin siyasa da sauransu ba sa tunanin cewa Ubangiji ne ke ba da arziki, Shi ya ba mu rai ma balle kayan rayuwa? Ai zumunta da Ubangiji (ta wurin yin addu’a) ta fi komai, kada mu dauki yin addu’a da hannu sake, mu dauke ta hanyar rayuwarmu a kullum, ta wurin yin haka kuma za mu ci nasara mu kuma samu kariyar Ubangiji.
Zabura 91:1-9 n acewa “Duk wanda ya je wurin Madaukaki zai zauna lafiya, duk wanda yake zaune a inuwar Mai iko duka, ya iya cewa Ubangiji, “Kai ne kariyata da mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare Ka nake dogara!” Hakika zai kiyaye ka daga dukan hadarurruka da ka ɓoye, daga kuma dukan miyagun cututtuka. Zai rufe ka da fika-fikanSa, za ka zauna lafiya a karkashinsu.  A amincinSa zai tsare ka, Ya kiyaye ka. Ba za ka ji tsoron hadarurruka da dare ba, ko fadawar da za a yi maka da rana, ko annobar da take aukowa da dare, ko mugayen da suke kisa da tsakar rana. Mutum dubu za su fadi daura da kai, dubu goma kuma za su fadi dama da kai, amma kai, ba za a cuce ka ba. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta  mugaye. Domin ka dauka Ubangiji Yake kiyaye ka, Madaukaki ne Yake tsaronka.” Idan har muka zama masu yin addu’a babu shakka Ubangiji zai kasance tare da mu zai kuma yi mana jagora.
Yin addu’a da naciya takan sa mu yi kusa da Ubangiji kamar yadda yake a cikin Littafin Zabura 145:18-19  “Yana kusa da dukan wadanda suke kira gare Shi, wadanda suke kiranSa da zuciya daya. Yakan biya bukatar dukan wadanda suke tsoronSa, Yakan ji kukansu, Ya cece su.” Rashin yin kusa da Ubangiji kan rinjayo Shaidan cikin rayuwar dan Adam, zumunci da Shaidan kuma yakan kai mutum ga hallaka, shi ya sa Ubangiji Ya umurce mu cewa kada mu fasa yin addu’a domin addu’a tana da iko sosai, idan ka zama mai yin addu’a Shaidan zai guje ka, ba zai samu zarafin cusa maka wasu miyagun tunani ba domin kana magana ne da Ubangijinka Wanda Ya fi shi (Shaidan) iko. Gama maganar Allah na cewa; Ishaya 41:10 “Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar komai ya firgita ka. Zan sa ka yi karfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.” To me ya fi wannan shaida daga wurin Ubangijinka? Akwai wani abin da ya fi wannan ba mu bege? Tunda yake ba abin da ya fi Ubangiji Allah girma da iko, Ya kai mu nemi fuskarSa a koyaushe cikin rayuwarmu kamar yadda Ya umurce mu mu yi – addu’a ba fasawa.
Mu dauki zarafi a kowace rana mu yi wa kasarmu addu’a don ci gaba ta kowane fanni da kuma zaman lafiya cikinta baki daya.
Bari Ubangiji Allah Ya ba mu ikon yin addu’a ba fasawa a koyaushe don mu girma cikin sanin ikonSa cikin rayuwarmu, amin.
Kolosiyawa 4:2 “Ku lazamci yin addu’a, kuna zaune a fadake a kanta sosai, tare da gode wa Allah.
Shalom.