Yin addu’a ba fasawa (2)

Ku rika yin addu’a ba fāsawa (1 Tasalonikawa 5:17)   Muna yi wa Ubangiji Allah godiya da Ya bar mu cikin rayayyu a wannan mako. A wannan mako da yardar Ubangiji za mu yi bincike ne a kan yin addu’a. Bari mu duba cikin Littafin Afisawa 6:18, “A koyaushe kuna addu’a da roko ta wurin […]

Yin addu’a ba fasawa (2)
Yin addu’a ba fasawa (2)

Ku rika yin addu’a ba fāsawa

(1 Tasalonikawa 5:17)

 

Muna yi wa Ubangiji Allah godiya da Ya bar mu cikin rayayyu a wannan mako.

A wannan mako da yardar Ubangiji za mu yi bincike ne a kan yin addu’a.

Bari mu duba cikin Littafin Afisawa 6:18, “A koyaushe kuna addu’a da roko ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matukar naci, kuna yi wa dukkan tsarkaka addu’a.”

Idan mun kula za mu cewa mutane da dama yanzu ba sa addu’a sai idan sun shiga wata damuwa ko suna bukatar wani abu. Littafi Mai tsarki na cewa mu rika yin addu’a ba fasawa; ko cikin dadi ko cikin wahala. Ai ba ma zuwa ganin iyayenmu don mun shiga wata matsala ko muna neman biyan bukata, amma don mu sada zumunci mu kuma ba su darajansu na iyaye har ma su ba mu shawarwari masu muhimmanci da dama da za su karfafa mu su kuma taimake mu. Hakan nan addu’a take, sada zumunci da Ubangiji da kuma ba Shi girmanSa da darajarSa. Wasu lokuta mukan bar matsalolin da muke ciki su hana mu yin addu’a, alhali kuwa a lokacin ne ya kamata mu yi addu’a da naci. Ubangiji Yakan bar wasu jarabobi don mu girma cikin saninSa, domin a duk lokucin da muka shiga damuwa Ubangiji Allah Yana so Ya ga ko za mu kira sunanSa ko ba za mu yi ba, shi ya sa Ya ce mu rika yin addu’a ba fasawa. Sai mu sani cewa ba ma rayuwar nan da ikon kanmu, ba za mu iya yin komai ba, in ba tare da yardarsa ba, saboda haka, kada mu bar damuwoyinmu su raba mu da Ubangiji da kuma sanin ikonSa, domin Yana da ikon cetonmu daga kowane irin yanayi da muka samu kanmu a ciki. Filibiyawa 4:6-7, “Kada ku damu da komai, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu’a da roƙo, tare da gode wa Allah. Ta haka salamar Allah, wadda ta fi gaban dukkan fahimta, za ta tsai da zukatanku da tunaninku ga Almasihu Yesu.” Mu sanar da Shi, Ubangiji Shi ne maganin komai, kada mu karaya idan har ba mu samu biyan bukata a lokacin da muke zato ba, gama hanyarSa da namu ba daya suke ba hakan nan shirinSa da namu sun bambamta. Irimiya 29:11-13; “Gama Na san irin shirin da Na yi muku, ni Ubangiji Na faɗa. Shirin alheri, ba na mugunta ba. Zan ba ku gabata da sa zuciya. Sa’annan za ku yi kira a gare Ni, ku yi addu’a a wuriNa, zan kuwa ji ku. Za ku neme Ni ku same Ni, idan kun neme Ni da zuciya ɗaya.” Ishaya 55:8-9 Ubangiji Ya ce, “TunaniNa ba kamar irin naku ba ne, al’amuraNa kuma daban suke da naku. Kamar yadda sammai suke can nesa da kasa, haka al’amuraNa da tunaniNa suke nesa da naku.” Shi ya sa za ka ga wadansu sun fada tarkon Iblis don neman biyan bukatunsu a daidai wannan lokaci da suke bukata misali, haihuwa, neman dukiya, neman matsayi a wurin aiki, nasara cikin siyasa da sauransu. Ba sa tunanin cewa Ubangiji ne ke ba da arziki, Shi Ya ba mu rai ma balle kayan rayuwa? Ai zumunta da Ubangiji (ta wurin yin addu’a) ta fi komai, kada mu dauki yin addu’a da hannu sake, mu dauke ta hanyar rayuwarmu a kullum, ta wurin yin haka kuma za mu ci nasara mu kuma samu kariyar Ubangiji.

Zabura 91:1-9 na cewa; “Duk wanda ya je wurin Madaukaki zai zauna lafiya, duk wanda yake zaune a inuwar Mai iko duka, ya iya ce wa Ubangiji, “Kai ne kariyata da Mai kiyaye ni! Kai ne Allahna, a gare Ka nake dogara!” Hakika zai kiyaye ka daga dukkan hadarurruka da ka boye, daga kuma dukkan mugayen cututtuka. Zai rufe ka da fika-fikanSa, za ka zauna lafiya a karkashinsu. AmincinSa zai tsare ka, ya kiyaye ka. Ba za ka ji tsoron hadarurrka da dare ba, ko fadawar da za a yi maka da rana, ko annobar da take aukowa da dare, ko mugayen da suke kisa da tsakar rana. Mutum dubu za su faɗi daura da kai, dubu goma kuma za su fadi dama da kai, amma kai, ba za a cuce ka ba. Da idonka za ka duba, Ka ga yadda ake hukunta wa mugaye. Domin ka ɗauka Ubangiji Yake kiyaye ka, Maɗaukaki ne Yake tsaronka.” Idan har muka zama masu yin addu’a babu shakka Ubangiji zai kasance tare da mu zai kuma yi mana jagora.

Yin addu’a da naci kan sa mu yi kusa da Ubangiji kamar yadda yake a cikin Littafin Zabura 145:18-19; “Yana kusa da dukkan wadanda suke kira gare Shi, waɗanda suke kiranSa da zuciya ɗaya. Yakan biya bukatar dukkan wadanda suke tsoronSa, yakan ji kukansu, ya cece su.” Rashin yin kusa da Ubangiji kan rinjayo Shaidan cikin rayuwar dan Adam, zumunci da Shaidan kuma yakan kai mutum ga hallaka, shi ya sa Ubangiji Ya umarce mu cewa kada mu fasa yin addu’a  domin addu’a tana da iko sosai, idan ka zama mai yin addu’a Shaidan zai guje ka, ba zai samiu zarafin cusa maka wasu miyagun tunani ba domin kana magana ne da Ubangijinka wanda ya fi shi (Shaidan) iko. Gama maganar Allah na cewa; Ishaya 41:10 “Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar komai ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.” To me ya fi wannan shaida daga wurin Ubangijinka? Akwai wani abin da ya fi wannan ba mu bege? Tunda yake ba abin da ya fi Ubangiji Allah girma da iko, Ya kai mu nemi fuskarSa a koyaushe cikin rayuwarmu kamar yadda Ya umarcemu mu yi – addu’a ba fasawa.

Mu dauki zarafi a kowace rana mu yi wa kasarmu addu’a don ci gabanta.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos