Yin addu’a domin wadansu 2
Barkanmu da sake saduwa a wannan makon inda za mu ci gaba da nazari a kan yin addu’a. A wannan karon, za mu ga dalilan da ya kamata mu yi wa wadansu addu’a. Idan muka koma makon farko cikin bincikenmu a kan yin addu’a, za mu ga cewa Littafi Mai tsarki na nuna mana muhimmancin […]
Barkanmu da sake saduwa a wannan makon inda za mu ci gaba da nazari a kan yin addu’a. A wannan karon, za mu ga dalilan da ya kamata mu yi wa wadansu addu’a. Idan muka koma makon farko cikin bincikenmu a kan yin addu’a, za mu ga cewa Littafi Mai tsarki na nuna mana muhimmancin yin addu’a da kuma albarkokin da ke tafe da ita, shi ya sa yana da kyau wadansu ma su samu wannan albarkoki ta wurin tunawa da su a duk lokacin da muke yin addu’a. Tunawa ko kuma sa wadansu cikin addu’a domin nuna kauna (ba tare da nunawa ko kuma gaya wa wani cewa za ka ko kana yi wa wani addu’a ba), da zuciya daya da ban-gaskiya kana kuma bidan nufin Ubangiji bisa bukatun wadansu, misali; marasa lafiya, matafiya, makwabta, shugabannin kasa da mazauna kasar da makamantansu ba tare da neman wani ya biya ka ba amma Ubangiji (domin Shi Ya san abin da kake yi Shi kuma Ya san zuciyar kowa) abu ne mai karbuwa a gaban Ubangiji.
Sai mu yi lura domin Littafi Mai tsarki bai koya mana yi wa wadansu addu’a da kudi ba kamar yadda mutane da dama ke yi a yau. Ubangiji Yana bukatar mu yi wa juna addu’a don kauna. A lokacin da Yesu Almasihu yana nan duniya ya yi warkarwa, ya tada mattattu, ya ciyar da mutane da dama ba tare da neman kudi ko kyauta a wurin jama’a ba amma saboda kauna, kaunar da ta kai ga mutuwa a kan giciye don fansarmu, ai ya kai mu yi koyi da wannan.
A bayyane yake idan har muna binciken Littafi Mai tsarki a koyaushe, gama Littafi Mai tsarki jagora ne ga duk wanda ke kaunar bincikensa; Zabura 119:105; MaganarKa fitila ce wadda za ta bi da ni, haske ne kuma a kan hanyata.” Rashin biciken Littafi Mai tsarki kuwa kan sa mutum ya zama jahili wajen sanin umurnin Ubangiji Allah. (Yusha’u 4:6, “Mutanena sun lalace saboda jahilci.Tunda yake sun ƙi ilimi, Ni ma na ki ku da zaman Firist dina.” Za ka iya yin bayarwa ko kyauta ga Ikilisiyar Ubangiji, ko ga fasto, ko zawararwa da marayu ko wani da Ruhun Ubangiji ya bisheka, wannan na dauke da albarkun Ubangiji kwarai da gaske, amma ba wai kana neman wani abu daga wurin Ubangiji sai ka ba da kudi ko ka karba domin a yi ko ka yi wa wani addu’a, wannan ba daidai ba ne.
Umarni ne daga wurin Ubangiji cewa mu rika tunawa da juna a cikin addu’a a koyaushe; Afisawa 6:18 “A koyaushe kuna addu’a da roko ta wurin ikon Ruhu bafasawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matukar na ci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu’a.” Yin haka na kara kaunar juna na kuma kawar da son kai (wato kamar ka yi shekara da shekaru kana rokon Ubangiji Ya biya maka (naka) bukatu, ba ka tunawa da ’yan uwanka, marayu, ko zawarwa ba).
Na biye, yin addu’a domin wadansu hanya ce ta nuna tabbacin kaunar Yesu Almasihu cikin rayuwarmu ta masu bi, yin haka kan karfafa rayuwarmu ta ruhaniyya a zaman Ikilisiyya daya cikin Almasihu.
Filibiyawa 2:1-4; “In akwai karfafawa a cikinAlmasihu, in dai da karfin rinjaye na kauna, in har da tarayyarku ga Ruhu, da soyayyarku da kuma tausayinku, to, albarkacinsu ku cika sa farin cikina da zamanku lafiya da juna, kuna kaunar juna, nufinku daya, ra’ayinku daya. Kada ku yi komai da son kai ko girman kai, sai dai da tawali’u, kowa yana maida dan uwansa ya fi shi. Kowannenku kada ya kula da harkar kansa kawai, sai dai ya kula har da ta dan uwansa ma.’
Bayan wannan idan muka dauki bukatun wadansu gaban Ubangiji, babu shakka albarkokinSa za su kasance tare da mu, Zai kuma (ta hanyoyin da suka sha bamban da yadda muke tsammani) maye mana gurbin abubuwan da muka rasa. Ayuba 42:10 “Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa’ad da ya yi addu’a domin abokansa, sai Ubangiji Ya mayar masa da ribin abin da yake da shi a da.”
Har ma magabtanmu, muna yi musu addu’a domin Ubangiji Allah Ya sa kaunarSa cikin zukatansu, Ya maye gurbin mugunta da nagarta. Matiyu 5:44; “Amma ni ina gaya muku, ku kaunaci magabtanku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a.” Luka 6:28; “ Ku sa wa masu zaginku albarka. Masu wulakantaku kuma, ku yi musu addu’a.”
Hakan nan kuma mukan iya hada kai a zaman Ikilisiyyar Ubangiji, muna yi wa juna addu’a muna kuma yafe wa juna don mu zo gaban Ubangiji da tsabtar rai, Shi kuwa zai karbi addu’armu. Yakubu 5:14-16; “In waninku yana rashin lafiya, to, sai ya kira dattawan Ikilisiyya su yi masa addu’a, suna shafa masa mai da sunan Ubangiji. Addu’ar ban-gaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya.Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa. Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifuffukanku, kuna yi wa juna addu’a, don a warkar da ku. Addu’ar mai adalci tana da karfi na iko kwarai da gaske.
Idan muka bincika rayuwar Yesu Almasihu har zuwa ga rayuwar almajiransa cikin Littafi Mai tsarki, za mu ga cewa Yesu ya koya wa almajiransa yin addu’a kuma ya umarce su da su rika yin addu’a ba fasawa, bayan mutuwarsa da tashinsa zuwa sama, almajiransa ba su fasa yin addu’a ba, suna kuma tunawa da juna cikin addu’a a koyaushe, cikin jin dadi, tsanani har kurkuku ba su fa sa yi waj una addu’a ba. Ayukan Manzani 12:5-17; “Sai aka tsare Bitrus a kurkuku, Ikilisiyya kuwa ta himmantu ga rokon Allah saboda shi… sai ga mala’ikan Ubangiji tsaye kusa da shi, wani haske kuma ya haskaka dakin, sa’an nan mala’ikan ya bugi Bitrus a kwibi, ya tashe shi, ya ce, “Maza, ka tashi.” Sai kuwa sarkar ta zube daga hannunsa. Mala’ikan ya ce masa, “Yi damara, ka sa takalminka.” Sai ya yi. Sai ya ce masa, “Yafa mayafinka, ka biyo ni.”… Da ya gane haka, ya je gidan Maryamu, uwar Yahaya wanda ake kira Markus, inda aka taru da yawa, ana addu’a. Za mu ga abubuwan al’ajibi idan muka hada kai muna yi wa juna addua’a.
Idan Ubangiji Allah Ya bar mu cikin masu rai, za mu ci gaba daga nan don mu gane muhimmancin yi wa juna addu’a.
Ubangiji Allah Ya ba mu ganewa, amin.