Yin Fim ba na rago ba ne – Mudassir M. Barumi

Mudassir Mohammed Barumi furodusa ne kuma mai kasuwancin fina-finan Hausa, ya yi bayanin yadda harkar fim take tafiya da kuma matsalolin da ya fuskanta a matsayinsa na furodusa kuma dan kasuwa. Ya yi hasashen yadda harkar fim za ta kasance a nan gaba. Tahirina a takaiceSunana Mudassir Barumi, an haife ni a garin Sakkwato. Na […]

Yin Fim ba na rago ba ne – Mudassir M. Barumi

Mudassir Mohammed Barumi furodusa ne kuma mai kasuwancin fina-finan Hausa, ya yi bayanin yadda harkar fim take tafiya da kuma matsalolin da ya fuskanta a matsayinsa na furodusa kuma dan kasuwa. Ya yi hasashen yadda harkar fim za ta kasance a nan gaba.

Tahirina a takaice
Sunana Mudassir Barumi, an haife ni a garin Sakkwato. Na yi makarantar firamare a Sakkwato, sannan na yi makarantar sakandare a Birnin Kebbi. A dai Birnin Kebbi na yi difloma a kwas din ‘Banking and Finance’ a kwalejin Waziri Umaru Polytechnic.
Yadda na fara fim
Bayan na gama diflomata ne sai na fara harkar fim a matsayin mai tsara labarin fim. Domin tun farko burina na zama marubuci.  Haka na rika samun furodusoshi ina fada musu ina so na rika rubuta musu labarai, daga baya dai na gane harkar sai mutum yana da jari. Wannan ya sanya na koma harkar siyasa ta lokaci kadan. A nan ma na fuskanci wadansu matsaloli, daga baya kawai na dawo harkar fim. Bayan na samo jari ne sai na dawo harkar gadan-gadan inda na fara shirya fina-finai.  Fim dina na farko shi ne ‘Dokta Nasir’.
Fina-finan da na shirya
Akwai ‘Garin So Nisa’ da ‘Adon Tafiya’ da ‘Zango’ da ‘Mai Gidana’ da ‘Maishunku’ da ‘Barista’ da ‘Shahuda’ da   ‘Sultan’ da ‘Sadauki’ da ‘Mai Ciki’ da sauransu.
Lakanin Barumi
Barumi lakanin mahaifina ne, kuma shi ne sunan da ‘yan gidanmu suke amfani da shi, wanda hakan ne ya sa sunan kamfanina ya zama Barumi Mobies. A fina-finaina na baya MYZ nake amfani da shi, daga baya kuma sai na koma Barumi Mobies.
Raja’a kan fim maimakon siyasa
Ka san ita rayuwa kowa yana da abin da yake sha’awa.  Harkar fim hanya ce da za ka iya isar da sakonka cikin kankanen lokaci. Ko a harkar fim din ma na fi son shirya fina-finan Musulunci.
Dalilin da ya sa na zama furodusa
A zahirin gaskiya aktin bai taba burge ni ba, ba wai don ba na so ba, a’a, ni dai bangarori uku ne suka fi burge ni; wadanda suka hada da: ba da umarni da shiryawa da kuma rubuta labari. Kodayake a yanzu ina kasuwancin fina-finai, za a shirya fim a kawo mini in saya, kuma ina kasuwancin fina-finaina.
kalubalen da na fuskanta a matsayin furodusa
Ina fuskantar matsalolin cikin gida ne, wato a industiri. Akwai lokuta da dama a wurin daukar fim da jarumai ko wani daga cikin wadanda muke fim da su suka samu rashin lafiya ko wani tsautsayi ya afka musu, dole na dauki nauyin komai. Babu yadda za a gama fim ba tare da wata matsala ta taso ba, shi ya sa ma nake ware wani kudi saboda irin hakan.
Matsalar barayin zaune
Tabbas mu ‘yan kasuwa kamar ni da Rabi’u Arrahuz da Sani Rambo mun fi fuskantar wannan matsala. Hakan ta sanya har wuraren da ba a shiga ma mukan je don mu kamo barayin zaune, saboda mun san ‘yancinmu. Wannan ta sanya nake kira ga masu kallo idan har suna sonmu da kuma son ci gabanmu, to su daina sayan fim din da barayin zaune suka gurza, idan suka ci gaba da saya kuma to gobe ba za mu yi ba, saboda bayan mun kashe kudinmu mun fitar da fim, sai kuma su rika sayan na barayin zaune, idan sun yi haka dole faduwa za mu yi har ta kai mun kasa ci gaba da shirya fina-finai ko kuma mu canza wani kasuwancin.
A zahirin gaskiya hukumar Copy Right ba sa yi mana aikin komai duk da irin makudan kudin da muke ba su. Tun da na fara harkar fim ban taba jin labarin ko ganin lokacin da ‘yan copy right suka fita kama barayin zaune ba. Akwai lokacin da muka gayyace su, inda muka fita aiki tare sai suka zagaya suka karbi kudin wadanda muka kama, inda daga baya suka sake su. Da muka tambaye su sai suka ce guduwa suka yi.
korafin sababbin marubuta
Idan ma wasu furodusoshi ba sa karbar labaran sababbin marubuta, to ni dai ina yi, duk industiri babu furodusan da ya kai ni fitar da sababbin marubuta, duk wurin da na ga mutumin da ya ce mini shi marubuci ne nakan saurare shi, saboda da rubutu na fara harkar fim. Idan ya same ni nakan ce masa ya kawo labarin, bayan na karanta idan labarin ya yi mini sai na karba, idan kuma akwai gyare-gyare sai na gyara masa, amma dai na fi so na ba marubuci labari ya rubuta mini, saboda na fi son fina-finan Musulunci. Na fito da sababbin marubuta kamarsu Bashir Marafa da Dauda Shafi’u Giwa wanda ya rubuta fim din ‘Attajiri’ da sauransu. Yanzu idan sabon marubuci ya zo mini zan iya ba shi labarin da zai rubuta mini, amma ni zan tsara masa fitowa-bayan-fitowa, zan ba shi labarin yadda ba zai sha wahala ba.
Hasashe a kan harkar fim
Za a samu arziki a harkar fim nan gaba, amma sai an hada da hakuri, sannan idan ‘yan fim su hada kansu.
Shawara ga ‘yan fim
Ina son ‘yan fim su guji shiga siyasa, hakan zai fi mana alheri, a baya ‘yan fim sun shiga siyasa sun kuma fuskanci barazanar kisa da duka da sauransu.  Idan kuma dan fim zai yi siyasa to ya kamata ya fito takara ba wai ya rika bin ‘yan siyasa ba. Ina da ra’ayin siyasa, zan kuma yi takara nan ba da dadewa ba.