Yin rikafin COVID-19 biyayya ne ga umarnin Annabi —Sheikh Halliru Maraya

Malamin ya ce yin allurar rigakafin cutar ba ya karya azumi.

Yin rikafin COVID-19 biyayya ne ga umarnin Annabi —Sheikh Halliru Maraya

Fitaccen Malamin Musulunci a Jihar Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya ce Musulmai na iya yin allurar rigakafin cutar COVID-19 yayin da suke yin azumi ba tare da azuminsu ya kare ba.  

Sheikh Maraya ya ce, wajibi ne a kowane Musulmi ya tabbatar an yi masa rigakafin cutar don yakar cututtuka masu yaduwa a cikin jama’a saboda hakan na da muhalli a Musulunci.

Malamin wanda ya tattauna da Sashen Hausa na BBC Hausa, ya ce “Zuwa yin rikafin cutar kamar yin biyayya ne ga umarnin Manzon Allah (SAW) saboda ya bukaci mu nemi magani da kare mu daga cutuka.

“Annabi (SAW) ya ce, Allah bai turo wata cuta a bayan kasa ba face sai da ya aiko da maganinta, ba a dauke cutar coronavirus cikin ba.”

A don haka ya bukaci daukacin Musulmi da su karbi rigakafin  kamar yadda suke bin umarnin Manzon Allah (SAW) kan amfani da magani.

“Ina kira ga dukkan Musulmin kasar nan da su halarci cibiyoyin karbar rigakafin a yi musu don magance yaduwar cututtuka a tsakanin Jama’a,” inji shi.

Ya ce, idan aka yi la’akari da adadin mutanen da suka karbi rigakafin a fadin duniya sama da mutane  miliyan 500, hakan na nuna yadda rigakafin yake aiki ba tare da cutarwa ba.