Yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada —Sheikh Ibrahim Khalil
Sheikh Ibrahim ya bayyana cewa yin Tahajjud a gida ya fi lada da alheri, kuma ba dole ba ne a tsawaita karatu ko a sauke Al-Kur’ani.
Fitaccen malamin addinin Musulunci na Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa yin Sallar Tahajjud a gida ya fi lada da alheri kuma ba dole ba ne a tsawaita karatu ko a sauke Al-Kur’ani a cikin sallar.
Malamin ya yi wannan bayanin ne a yayin da al’ummar Musulmi suka dukufa wajen yin ibada a dararen kwanaki 10 na karshen watan Ramadan da aka shiga yanzu.
- Mahaifin tsohuwar jarumar Kannywood Muhibbat Abdussalam ya rasu
- Ramadan: Gidauniyar Dangote ta raba buhunan shinkafa miliyan ɗaya a bana
“Mutum ya yi Sallar Tahajjud a gida ya fi alheri, ya fi albarka ya fi lada,” in ji Sheikh Ibrahim Khalil, a wata hirar da ya taba yi da Freedom Radio.
A dararen kwanaki 10 na karshen watan Ramadan ne dai Musulmi suka fi dukufa wajen yin ibada, inda suke yin fitar dango maza da mata zuwa masallatai da tsakar dare domin yin Sallar Tahajjud da neman dacewa da Daren Daraja (Lailatul Kadari).
Akasari ana sauke Al-Kur’ani a kwanaki 1o da ake yin a sallar tahajjud inda ake karanta izu shida a kowane dare.
Irin wannan jajircewa na da nasaba da irin kwadaitarwar da malamai suka yi game da falalar sallar da falalar daren Lailatul Kadari; Uwa uba, koyi da Manzon Allah (SAW) wanda a dararen yakan ninninka yanayin yadda yake ibada tare da karfafar iyalansa su yi hakan.
A kan haka ne Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa idan mutum ya yi Sallar Tahajjud a gida ta fi lada kuma ya fi alheri.
“Mutum ya yi Sallar Tahajjud a gida ya fi alheri, ya fi albarka ya fi lada,” in ji Sheikh Ibrahim Khalil, a hirarsa Freedom Radio.
Inda Tahajjud a masallaci ya fi lada
Sai dai ya bayyana cewa akwai yanayin da yin sallar ta Tahajjud a masallaci ya fi lada ga mutum.
A cewarsa malamain, mutumin da ba zai iya yi shi kadai ba, ko kuma “ba shi da karfin zuciyar da zai iya yi shi kadai ko kuma ba zai iya samun nutsuwa ba, sai ya zo masallaci cikin jama’a, to shi kuma ya zo a cikin jama’a ya fi lada.”
Amma mutumin da “idan ya yi a gidansa zai fi samun nutsuwa, to ya yi a gida ya fi lada; wanda kuma ya san ba zai yi sakaci ba, zai iya tashi ya yi, to ya yi a gida ta fi lada, kamar yadda Sayyiduna Umar (RA) ya fada, kamar yadda Annabi (SAW) ya yi.”
Amfanin Sallar Tahajjud
Malamin ya ce daga cikin amfanin sallar akwai kara wa mutum kusanci da Allah, da taimawa wajen samun tsarkin zuciya kuma tana gyara tunanin dan Adam
Ba dole sai an sauke Al-Kur’ani ba
Ya bayyaan cewa ba dole ne a sauke Al-Kur’ani a sallar ta Tahajjd ba, amma dai ana yin haka ne domin neman lada.
“Wannan sauka da mutane suke yi sha’awa ce suka dora wa kansu, saboda haka idan sun yi babu laifi, idan ba su yi ba babu laifi.
“Kuma ba laifi ba ne a yi ta karanta aya daya ko sura da ko wasu wurare” kadai a yayin sallar, kamar yadda ya bayyana.
Abin tsawaita karatu a Tahajjud
A game da yanayin karatu a Tahajjud, shugaban Majalisar malaman ya bayyana cewa, duk da cewa abin da ake so shi ne tsawaita karatu, amma ya danganta ne da yanayin mamu.
Ya ce abin da aka fi so a yawan sallar nafilar rana shi ne yawan raka’o’i, amma a sallar dare kuma an fi son yawan tsayuwa da karatu.
“Amma dukkansu sun danganta da yanayin mamu, domin Annabi (SAW) idan ya fahimta mutane suna cikin kunci, to yakan gajarta sallah; in kuma ya fahimci suna cikin nishadi yakan tsawaita,” in ji Malam Ibrahim Khalil.
Ya ce saboda haka abin da ake bukata daga limami shi ne lura da yanayin mamunsa, “Idan mamunsa suna son tsawaitawa sai ya tsawaita, idan suna son gajartawa sai ya gajarta, idan kuma tsakaitawa ne sai ya tsakaita.”