Yiwuwar ɓarkewar cuta: An gargaɗi ’yan Maiduguri kan sayen kayan lambu
Gwamnatin Borno ta gargadi mazauna wuraren da ambaliya ta shafa su guji sayen kayan lambu da kayan gwari a yankunan.
Gwamnatin Borno ta gargadi mazauna yankunan da aka samu ambaliya da su guji sayen kayan lambu da kayan gwari a yankunan nasu.
Wani sakon kar-ta-kwana da gwamnatin jihar ta fitar ranar Talata ta ce akwai yiwuwar barkewar cututtuka masu alaka da gurbacewar ruwa a sakamkon ambaliyar.
“A sakamakon ambaliyar, akwai yiwuwar kayan lambu a yankunan da abin ya shafa sun gurbace da abubuwa masu hadari kamar ruwan kazantar dan Adam, gawarwaki, sinadaran masana’antu, kwayoyin cuta da wasu abubuwa masu guba.
“Saboda haka cin kayan lambu da aka samar a irin wadannan yankuna na da hadarin gaske ga lafiya, domin za a iya kamuwa da cututtuka masu alaka da gurbataccen ruwa ko harbuwa da gubar abinci da saura matsaloli.”
- Tinubu ya fi ƙarfin satar dukiyar Najeriya — Minista
- Aminu Dantata ya ba mutanen Maiduguri tallafin N1.5bn
- Biliyan N250 Matawalle ya wawushe a Zamfara —Dauda Lawal
Sanarwar da Ma’aikatar Watsa Labarai da Tsaron Cikin Gida ta fitar ta ci gaba da cewa, “Domin kare rayuwarku da lafiyarku, muna kira gare ku:
“Guji sayen kayan lambu da aka noma a wuraren da aka samu ambaliya, ku tabbata kun saye ne daga amintattun wurare da kasuwanni
“Sannan ku tabbatar kun wanke su sosai, yadda ya kamata kafin ku yi amfani da su.”
Sanarwar mai dauke da sa hannun Farfesa Asheikh LG, ta ce “A irin wannan yanayi da muka tsinci kanmu, yana da matukar muhimmaci mu ba da fifiko ga duk abin da ya shafi lafiyarmu da kare rayuwarmu.“