Yiwuwar yin kare jini biri jini a zaben 2019

A halin yanzu dai dukan jam’iyyu sun kammala zaben fid da gwani domin fitar da wadanda za su tsaya takara a zaben shekarar 2019 da za a yi, abin da ya rage kawai sai hasashen da ake yi game da jam’iyyar da za ta lashen zaben. Kamar yadda aka sani manyan jam’iyyun APC da PDP sun […]

Yiwuwar yin kare jini biri jini a zaben 2019
Yiwuwar yin kare jini biri jini a zaben 2019

A halin yanzu dai dukan jam’iyyu sun kammala zaben fid da gwani domin fitar da wadanda za su tsaya takara a zaben shekarar 2019 da za a yi, abin da ya rage kawai sai hasashen da ake yi game da jam’iyyar da za ta lashen zaben.

Kamar yadda aka sani manyan jam’iyyun APC da PDP sun fitar da ’yan takarar shugabancin kasar nan, inda Jam’iyyar APC mai mulki ta tsayar da Shugaba Muhammadu Buhari, ita kuma Jam’iyyar PDP ta tsayar da Wazirin Adamawa Atiku Abubakar a matsayin dan takararta, a yayin da jam’iyyar SDP ta tsayar da tsohon Gwamnan Jihar Kuros Ribas Donald Duke a matsayin dan takararta.

Sai dai kuma wadansu na ganin tsayar da Atiku da Jam’yyar PDP ta yi a matsayin.dan takarar Shugaban Kasa kamar zai ba Shugaba Buhari na APC damar  tsintar dame a kala ne, saboda suna ganin Atiku ba zai iya ja da Buhari ba. Amma kuma wadansu na ganin an ballo wa Shugaba Buhari aiki ne domin Atiku ba kanwar lasa ba ne a siyasar Najeriya.

Kokarin da ake yi domin shafa wa Atiku kashin kaji ta hanyar danganta shi da rashin gaskiya ana ganin hakan zai taimaka wa Buhari, domin ana tunanin idan Atiku ya karbi ragamar shugabancin kasar nan zai zubar da mutuncinta. Kuma ana ganin yakin da Buhari yake yi da rashawa zai kawo karshe a gwamnatin Atiku, saboda zai kyale miyagun mutane su yi rawar gaban hantsi.

Amma shi Atiku ya sha bayyana cewa shi  ba maha’inci ba ne kuma ba mutum ne da zai daure wa rashin gaskiya gindi ba. Sannan akwai masu kukan cewa su ba su gane yaki da rashawa da cin hanci da Buhari yake yi ba alhali ya bar su suna kwana da yunwa. Wannan ya sanya ake ganin Atiku  zai iya yin amfanin da halin matsin da talakawa ke ciki a halin yanzu domin ya lasa musu zuma a baki ta hanyar yi musu alkawarin samun sassauci game da matakan farfado da tattalin arziki da wannan gwamnatin ta filto da su.

Haka kuma ana ganin akwai abubuwa da dama da za su haifar wa Buhari tarnaki sakamakon zaben da PDP ta yi wa Atiku a matsayin dan takarar Shugaban Kasa, misali, ’yan sabuwar PDP din nan, wadanda jiga-jigai ne da suka kunshi shi kansa Atiku da Bukola Saraki da Rabi’u Musa Kwankwaso da Aminu Tambuwal da sauransu, wadanda suka fice daga Jam’iyyar PDP a shekarar 2015 suka koma APC kuma suka taimaka wa Buhari ya ci zabe, yanzu da yake sun sake komawa PDP za su ci gaba da yin tasirin da zai iya girgiza Buhari. Saboda kowannensu yana da dimbin magoya baya da dulk inda ya sanya gaba nan za su bi.

Akwai kuma wadanda aka bata wa rai sakanakon manufofin da wannan gwamnati ta fito da su, irin wadannan mutanen suna nan sun yi lambo suna jiran ranar da za su dauki fansa. Hatta gwamnonin APC  ma akwai wadanda Buhari ya bata musu rai a yayin zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC din.

Akwai kuma ’yan kungiyar Shi’a, wadanda a baya ake cewa ba su damu da yin zabe ba, amma a wannan karon an ce sun karbi katin zabe da nufin kawar da gwamnatin Buhari saboda cin mutuncin da suke gani gwamnatinsa ta yi musu.

Haka kuma a shekarar 2015 Buhari ya samu gagarumin goyon bayan daga yankin Kudu maso Yamma (kasar Yarbawa), amma ana ganin a wannan karon da dama daga cikinsu sun dawo daga rakiyarsa, za a fahimci haka ne idan aka yi la’akari da yadda zabubbukan jihohin Ekiti da Ondo da Osun  suka gudana, wadannda suka nuna cewa Jam’iyyar PDP ta farfado a yankin. Wannan ya nuna cewa samun cikakken goyon baya ga Buhari irin na shekarar.2015 a kasar Yarbawa zai yi wuya a wannan karo.

A shekarar 2015 an yi taron dangi ne aka kori  Jonathan saboda ana ganin kasar ta gagare shi rikewa, domin baya ga wadanda suka yake shi a wajen jam’iyya, hatta wadanda suke cikin Jam’iyyar PDP  ma sun yake shi. Sai dai kuma duk da wannan taron dangin da aka yi wa Jonathan a wancan lokacin bambacin kuri’arsa da ta Buhari ba mai yawa ne sosai ba.

A sauran yankunan kasar ma Buhari zai iya fuskantar matsala, saboda kamun ludayinsa a harkar gwamnati ya sanya wadansu mutane da dama dawowa daga rakiyarsa, domin lokacin da suka zabe shi sun dauka al’amura za su daidaita nan da nan, amma sai suka wayi gari harkoki sun rikice musu. Rahotanni sun nuna cewa Atiku ya samu kuri’a da yawa daga wakilan yankinsa na Arewa maso Gabas a Fatakwal, wannan ya nuna cewa zai iya samun goyon baya daga wannan yanki, musamman da yake akwai masu guna-gunin cewa yankin bai taba yin Shugaban Kasa ba, yankin Arewa ta Yamma ne yake ta samar da shugabanni, to yanzu suna ganin dama ta samu.

Tunanin da wadansu ke yi cewa zaben da aka yi wa Atiku a matsayin dan takarar Shugaban Kasa wata dama ce ta samun nasara ga Shugaba Buhari cikin sauki yana iya zama babban kuskure, domin siyasa ’yar zamba ce, dan siyasa zai yi amfani da hanyoyi da dama domin yacimma burinsa.

Yayin da ake ganin akwai abubuwan da za a yi amfani da su da dama a raunata Atiku a yayin yakin neman zabe, haka shi ma Atiku da magoya bayansa suna da abubuwan da za su yi yakin neman zabe da su da za su bata gwamnati domin su kai ga kwace gwamnati daga hannun Shugaba Buhari. Hausawa na cewa dan hakin da ka raina shi ke tsone maka ido.

A wannan karon saboda duk  ’yan takarar daga yankin Arewa suke kuma addininsu daya ne, babu batun buga kugen jihadi, domin haka wadansu ba za su fita su yi zaben ba, za su ce duk wanda ya ci nasu ne.