Yobe: Ɗan majalisa mai hawa bakwai ya zama shugaba
Daga Habibu Idris Gimba, Damaturu Majalisar Dokokin jihar Yobe ta zaɓi ɗan majalisar da yafi kowa daɗewa akan kujera a matsayin shugabanta. Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta zaɓi wakilin mazaɓar Jajere dake ƙaramar hukumar Fune, Buba Chiroma Mashiyo wanda tun 1999 yake kan kujerarsa. Wato dai ya shekara 24 a Majalisar kuma ya yi […]
Daga Habibu Idris Gimba, Damaturu
Majalisar Dokokin jihar Yobe ta zaɓi ɗan majalisar da yafi kowa daɗewa akan kujera a matsayin shugabanta.
Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar ta zaɓi wakilin mazaɓar Jajere dake ƙaramar hukumar Fune, Buba Chiroma Mashiyo wanda tun 1999 yake kan kujerarsa.
Wato dai ya shekara 24 a Majalisar kuma ya yi nasarar cin zaɓe sau bakwai.
Matashi ya kera motar ‘A kori kura’ a Yobe
Shugaban karamar hukuma ya rasu ana dab da rantsar da shi a Yobe
Wakilin Mazaɓar Karasuwa, Adamu Dala Dogo ne ya bada sunansa a matsayin ɗan takara yayin da wakilin mazaɓar Geidam ta Tsakiya, Bukar Mustapha Timba ya mara masa baya.
Ƴan Majalisar sun kuma zaɓi Ya’u Usman Dachia mai wakiltar mazaɓar Jakusko a matsayin mataimakin shugaba.