Yobe da Barno: Mu tuna da Shehu El-Kanemi?

Editan Amintacciyar jarida, ka ba ni dama in yi wa al’ummar Jihohin Yobe da Barno tuni kan lallai su nemo wani Shehu irin Marigayi Shehu Mustapha el-Kanemi, don warware matsalolin rikicin addini da kabilanci da ke addabar yankin Arewa maso Gabas, al’amarin da kodayaushe ake ta’allaka shi ga Boko Haram. A hakikanin gaskiya wadanda ake […]

Yobe da Barno: Mu tuna da Shehu El-Kanemi?

Marigayi Shehu Mustapha el-KanemiEditan Amintacciyar jarida, ka ba ni dama in yi wa al’ummar Jihohin Yobe da Barno tuni kan lallai su nemo wani Shehu irin Marigayi Shehu Mustapha el-Kanemi, don warware matsalolin rikicin addini da kabilanci da ke addabar yankin Arewa maso Gabas, al’amarin da kodayaushe ake ta’allaka shi ga Boko Haram. A hakikanin gaskiya wadanda ake fada da su a wannan yanki ’ya’yan mutanen wannan yankin ne, don haka ina iyayensu da malmansu? Idan har akwai, kamata ya yi su tsawatar musu, don shawo kan rikici, amma sai aka kyale al’amari ya cabe, har ta kai ga an kawo sojoji suna yin kan mai uwa da wabi.
Zan iya tunawa a lokacin da Shehun Barno, Mustapha el-Kanemi na da rai, wata rana, Marigayi Muhammad Yusuf ya taba cewa ba zai yi sallar idi da mutanen gari ba, don haka hukuma ta yi yunkurin hana shi, amma da el-Kanemi ya samu labari sai ya aika aka kira shi, ya ce masa, “dana ka ce ba za ka yi sallar idi da sauran al’umma ba,” shi kuwa ya amsa masa “e,” sai ya ce ka je ka yi. Saboda irin masalahar da ya saba yi a tsakanin al’umma, har el-Kanemi ya bar duniya ba a cika samun mummunan rikici a Barno da Yobe kamar yadda muke fama da shi a irin wannan lokacin ba. Babban sirrin nasarar Shehu wajen warware matsalolin al’umma, shi ne rashin nuna bambanci tsakanin bare-bari da sauran kabilu, don ko wanda ba Musulmi ba, idan ya zo wajen Shehu za a yi masa adalci, har ma in ta kama a yi masa taimakon duk da ya dace.
Mutanen Barno da Yobe, lokaci ya ya yi da kowa zai kokarin fin karfin gidansa, ta hanyar daukar nauyin iyali da tarbiyyar ’ya’ya, uwa-uba tsawatar musu a kan duk abin da a ka ga b a daidai ba ne.
Rashin manya ko masu kwatanta dabi’u na dattako irin na shehu Mustapha el-Kanemi ba karamar asara ba ce ga kasar nan, domin Kirista da Musulmi suna zaman lafiya, amma wasu ’yan tsirarin masu son rai ke cusa gaba da kiyayya, har ta kai ga sun haddasa fitina da ruruta wutar rikici.
Kai koda su Hamza al-Mustapha da Muhammad Abacha da suka shiga kurkuku, ni ina ganin ‘yan arewa suka yi musu sharri, don haka matsalarmu ba ta Kudu da Arewa ba ce. Koda kuwa mun ga shugabanni na nuna bambanci. Kusan kowa yasan yadda Katako ya yi ikrarin yi wa al-Mustapha sharri; ga kuma Sajen Rogers, wadanda duk bincike ya nuna kudi aka ba su, suka aiwatar da manufofin son ransu. Katako dan Biniwai ne, shi kuwa Rogers dan adamawa ne. Don haka sai mu tambayi kanmu; ’yan kudu ke yi mana illa, ko kuwa ’yan Arewa ne ke cin dunduniyar yankinsu?
Amsar tambayar da aka bijiro da ita, lallai ’yan Arewa su daina cin dunduniyar junansu; a yi wa kowa adalci. Uwa-uba a gyara ilimi da tarbniyyar al’umma. Yin haka zai sanya bambancin addini ko na kabilanci ba zai yi tasiri ba. Domin ko a zamanin sahabbai an samu sabanin fahimtar hukunce-hukuncen fikihu da karatun Littafin Allah, amma ba su bari wannan ta raba kan al’umma ba. Duk da cewa muna da firkoki na addini daban-daban, wajibi ne mu yi kawunanmu kiyamul laili, tunda an taso musulmi a ko’ina cikin duniya. Mu fara yi wa kawunanmu adalci, kafin duniya ta yi mana. Musulunci addinin zaman lafiya ne, mu nemi maslaha ko Allah Ya ba mu salama.
Matukar wannan al’ummar naso a wanye lafiya, to wajibi ne shugabanni su yi adalci, ta yadda za a rika ganinsu da kima. Kuma da an hango wata fitina ta kunno kai, a yi saurin kashe wutarta, don kada ta yi ta ruruwa. Shugabanni da mabiya, mu daina yin taron shan shayi, inda a kulum muke kiran sunan Ahmadu Bello Sardauna, amma ba ma kokarin koyi da kyawawan dabiunsa, wadanda suka hada da rashin nuna wariyar kabilanci da bambancin addini, tamkar yadda mutanen Barno da Yobe suka san Shehu el-Kanemi ya kwatanta. Don haka kalubale a garemu: mu himmatu wajen mika jagorancin al’umma a hannun mutane masu kyawawan dabi’u da zimmar tabbatar da adala irin na Sa Ahmadu Bello Sardauna da Shehu Mustapha el-Kanemi, kai har ma da daukacin mutanen kwarai wadanda suka wanzu a cikin tarihi, ta yadda za mu samu mafita daga bala’o’in da suka baibaye al’umma. Allah Ya yi mana muwafaka.
Maigari ya rubuto makalarsa daga Abuja.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna