Yobe ta ba da tabbacin kariya ga daliban makarantun jihar
Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da tabbaci ga iyayen yara cewa ta daura damarar ba da kariya ta musamman ga rayukan yaransu da ke makarantun sakandaren jihar, ta hanyar ba da karfin gwiwa ga jami’an tsaro su fuskanci kalubalen tsaron makarantu da a baya suka yi fama da hare-haren ’yan bindiga.Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji […]
Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da tabbaci ga iyayen yara cewa ta daura damarar ba da kariya ta musamman ga rayukan yaransu da ke makarantun sakandaren jihar, ta hanyar ba da karfin gwiwa ga jami’an tsaro su fuskanci kalubalen tsaron makarantu da a baya suka yi fama da hare-haren ’yan bindiga.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Alhaji Muhammad Lamin ne ya bayana haka a jawabinsa ga manema labarai a gidan gwamnatin jihar kan kokarin gwamnatin jihar na sake bude makarantun sakandare da firamaren jihar domin fara karatun zangon farko na shekarar karatu ta 2013/2014.
Kwamshinan ya ce, kare rayukan daliban ya zama wajibi kasancewarsu amana ne a hannunsu, “don haka akwai bukatar da iyaye da al’ummar jihar su ci gaba da bada goyon baya ga jami’an tsaro ta wajen bada rahoton duk wadanda ba su yarda da take-takensu ba,” inji shi.
Ya umarci shugabannin makarantun sakandare da firamare na gwamnati da masu zaman kansu su gaggauta bude su don fara karatu. Kuma ya nemi shugabannin makarantun sakanadare da dalibai su rika taimaka wa jami’an tsaro ta tona asirin batagari da ke kokarin shiga huruminsu.
Alhaji Lamin ya ce makarantu biyu da suka hadu da harin ’yan bindiga a garuruwan Damaturu da Mamudo ba za a bude su ba sai bayan mako biyu, saboda ana sake gyara inda ’yan bindigar suka kona su.