Yobe Ta Fara Rijistar Makiyaya Aikin Hajjin 2027
Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman, ya sanar da cewa, an sanya kuxin farko na Naira miliyan 7.5
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni
https://aminiya.ng/a-kurkura-guba-ko-magani/
Yobe Ta Fara Rijistar Aikin Hajjin 2027
Daga Sani Saleh, Chinade Damaturu
Shugaban Hukumar Alhazai ta Jihar Yobe, Alhaji Mai Aliyu Usman, ya sanar da cewa, an sanya kuxin farko na Naira miliyan 7 da dubu 500 (N7.5M) don aikin hajjin 2027.
Ya sanar da hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar hukumar da ke Damaturu.
Mai Aliyu ya jaddada cewa, watanni uku kacal suka rage don rufe ci gaba da yin rijistar mahajjata, bisa umarnin da Hukumar Hajji ta Qasa (NAHCON) da masarautar Saudiyya suka bayar, waxanda suka sanya ranar rufe rajistar a watan Satumba, 2026 ga mahajjata a faxin duniya.
- Ya jaddada cewa, duk wanda ke son zuwa aikin hajji na shekarar 2027, dole ne ya bi hanyar biyan kuxi ta hanyar ajiye kuxi ba tare da wani sharaxi ba. Kuma ya kamata a aiwatar da biyan kuxi ne kawai ta hanyoyin da aka ba da izini ta hannun jami’an da aka naxa a hedikwatar hukumar da masu karvar kuxin hajji na qananan hukumomi da aka ba da izini.
Ya gargaxi jama’a game da ba da kuxi ga mutanen da ba ma’aikatan hukumar tare da alqawarin sauqaqe musu bin hanyoyin biyan kuxin aikin hajjin.
Yana jaddada cewa, duk wanda aka samu yana aikata irin waxannan ayyukan ba bisa qa’ida ba zai fuskanci hukuncin da ya dace da shi.
Ya kuma jaddada cewa kuxin aikin hajji na qarshe na 2027 na iya bambanta da na 2026, yana mai qara da cewa, masu niyyar zuwa aikin hajji su qara haquri don jira kuxin hukuma da hukumomin Saudiyya za su sanar a qarshen wannan shekarar a matsayin qarshen wa’adin.
Mai Aliyu, ya kuma shawarci mahajjatan da fasfo xinsu na qasashen waje ya kusa qarewa da su sabunta su da sauri don guje wa jinkiri ko matsaloli wajen samun biza.
Shugaban ya yi kira ga jami’an yankin da su kasance masu taka tsantsan, su tabbatar da cewa, an cika dukkan kujerun aikin hajji, sannan kuma ya wayar da kan jama’a game da kammala rajistar su kafin wa’adin ya cika.
Bugu da qari, Mai Aliyu ya miqa godiyarsa ga gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, saboda ci gaba da samun cikakken haxin kai da goyon baya da hukumar ke samu a duk lokacin aikin hajji.