Yobe ta kafa kwamitin ko-ta-kwana kan rigakafi
Gwamnatin Jihar Yobe da hadin gwiwar Gidauniyar Bill and Melinda Gates da kuma Gidauniyar Dangote sun dukufa don gudanar da aikin rigakafin cututtukan da suke addabar yara.Bayanin haka ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam a yayin kaddamar da kwamitin ko-ta-kwana kan rigakafin cututtukan da suke addabar yara a matakin farko na […]
Gwamnatin Jihar Yobe da hadin gwiwar Gidauniyar Bill and Melinda Gates da kuma Gidauniyar Dangote sun dukufa don gudanar da aikin rigakafin cututtukan da suke addabar yara.
Bayanin haka ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam a yayin kaddamar da kwamitin ko-ta-kwana kan rigakafin cututtukan da suke addabar yara a matakin farko na kananan hukumomin jihar da aka gudanar a dakin taro na Sakatariyar Jihar da ke garin Damaturu.
Gwamna Gaidam wanda Mataimakinsa Injiniya Abubakar Ali ya wakilta ya kara da cewa, gwamnatin jihar tana yin duk abin da ya wajaba domin ganin ta inganta harkokin kiwon lafiya a jihar musanman ganin cewa cututtuka da dama masu kisa farat daya na kara yawaita, kuma hakan babbar barazana ce ga al’umma.
Ya ce samar da hanyoyin rigakafin cututtukan ne babban abin yi ga gwamnati don tserar da rayukan al’ummar jihar ta wajen kiyaye kamuwa da kwayoyin cututtuka masu addabar jama’a. Sai ya bukaci ’yan kwamitin su gudanar da ayyukan da aka dora musu bil-hakki da gaskiya don a cimma muhimman manufofin kafa kwamitin tare da inganta kiwon lafiya a jihar.