Yobe ta kasafta Naira biliyan 102 a bana
Gwamnatin Jihar Yobe ta kasafta Naira biliyan 102 da miliyan 899 da dubu 142, a matsayin kasafin kudin bana, hakan ya nuna an samu karin sama da Naira biliyan 16 da miliyan 240 a kan kasafin kudin bara koa kashi 15.7 cikin 100. Da yake gabatar da kasafin gaban Majalisar Dokokin Jihar a Damaturu, Gwamnan […]
Gwamnatin Jihar Yobe ta kasafta Naira biliyan 102 da miliyan 899 da dubu 142, a matsayin kasafin kudin bana, hakan ya nuna an samu karin sama da Naira biliyan 16 da miliyan 240 a kan kasafin kudin bara koa kashi 15.7 cikin 100. Da yake gabatar da kasafin gaban Majalisar Dokokin Jihar a Damaturu, Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam ya ce kasafin na bana an yi masa lakabi da kasafin samar da abubuwan more rayuwar al’umma da kuma inganta tattalin arzikin jiha, ya ce a kasafin na bana gwamnati na da kudirin gudanar da ayyuka masu muhimmanci tare da karasa sauran ayyukan da aka fara da kuma aiwatar da sababbin ayyuka da suka hada da gina sababbin hanyoyin mota a kowane bangaren jihar da inganta ilimi da harkokin kiwon lafiya da sauransu. Ma’aikatun da suka fi samun kaso mai tsoka sun hada da Ma’aikatar Ayyuka wacce ta tashi da Naira biliyan 16 da miliyan 279 da dubu 280, sai Ma’akatar Ilimi da ta zo ta biyu da Naira biliyan 8 da miliyan 643 da dubu 423.