Yobe ta mika mutum 158 da ’yan Boko Haram suka sako ga iyalansu

Gwamnatin Jihar Yobe ta mika kimanin mutum 158 da suka hada da mata da yara da ’yan Boko Haram suka yi awon gaba da su a harin da suka kai a kauyen Katarko a karamar Hukumar Gujba kuma suka sako su kimanin mako uku da suka gabata ga iyalansu tare da ba su tallafin kayan […]

Yobe ta mika mutum 158 da ’yan Boko Haram suka sako ga iyalansu
Yobe ta mika mutum 158 da ’yan Boko Haram suka sako ga iyalansu

Gwamnatin Jihar Yobe ta mika kimanin mutum 158 da suka hada da mata da yara da ’yan Boko Haram suka yi awon gaba da su a harin da suka kai a kauyen Katarko a karamar Hukumar Gujba kuma suka sako su kimanin mako uku da suka gabata ga iyalansu tare da ba su tallafin kayan abinci da kudi.

Da yake jawabi ga iyalan mutanen a garin Damaturu shugaban kwamitin kula da mutanen da aka sako Kwamishinan Shari’a na Jihar Ahmed Mustafa Goniri ya ce gwamnatin jihar ta ji dadin samun kansu da suka yi kuma ta tallafa musu ne don rage musu wahalar rayuwa kasancewar galibinsu mata ne da aka kashe mazajensu tare yaran da suka rasa iyayensu.
Ya yi fatan wadanda aka mika musu ’yan uwansu za su kula da su tare da ci gaba da kwantar musu da hankali ya kuma nuna godiyar gwamnatin jihar ga jami’an tsaro kan yadda suka kula ga mutane a tsawon zaman da suka yi a hannunsu kafin mika su ga gwamnati.
Shugaban kwamitin ya ce gwamnatin jihar ta bada tallafin buhun shinkafa biyu da buhun siga daya katon biyu na taliyar indomi da buhun gishiri daya da turamen zannuwa biyu ga kowace mace daga cikin mata 60 da suka kubuta ta kuma bada Naira dubu 50 ga kowace daya daga cikin mata 15 da suka rasa mazajensu a cikin harin da aka kai garin nasu.
Ya ce har ila yau gwamnatin ta bada tallafin Naira dubu 30 ga sauran mata 47 don rage musu radadin rayuwa.
Da Aminiya ke jin ta bakin Hauwa Muhammad daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin ta ce sun yi matukar farin cikin samun kansu daga hannun ’yan Boko Haram kuma ta mika godiyarta ga gwamnatin jihar kan kulawa da su da ba su tallafin kayan abinci da kudi.