Yobe ta tallafa wa ’yan gudun hijira da buhunan abinci 650
Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da tallafin kayan da kudinsu ya kai Naira miliyan 15 ga ’yan gudun hijirar da suke tsugunne a karamar Hukumar Karasuwa don rage musu kuncin rayuwa da hare-haren ’yan Boko Haram ya jefa su a ciki.’Yan gundun hijirar dai sun baro garuruwansu na asali ne daga jihohin Yobe da Borno […]
Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da tallafin kayan da kudinsu ya kai Naira miliyan 15 ga ’yan gudun hijirar da suke tsugunne a karamar Hukumar Karasuwa don rage musu kuncin rayuwa da hare-haren ’yan Boko Haram ya jefa su a ciki.
’Yan gundun hijirar dai sun baro garuruwansu na asali ne daga jihohin Yobe da Borno da Adamawa.
Da yake mika kayan tallafin ga Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SERA), Sakataren Gwamnatin Jihar, Injiniya Baba Goni Machina ya ce kayan agaji za a raba su ne kawai ga al’ummomin da hari rikicin ’yan bindiga ya shafa da suka yiwo hijira daga garuruwan Kirenewa da Bama da Kondiga da Baga da Maiduguri da Talala da Damboa a Jihar Borno da kuma wadanda suka fito daga Buni Gari da Yadin Buni da Goneri da Bumsa da Bara da sauransu daga Jihar Yobe.
Kayayyakin da gwamnatin ta ba da sun hada da buhhunan gero 200 da na shinkafa 250 da na masara 200 da katan din taliyar Indomie 350 da jarkokin man girki 170. Sauran sun hada da buhun gishirin 310 da gidan sauro 360 da tabarmi 360.
Injiniya Baba Goni Machina ya ce wannan tallafi na karamar Hukumar Karasuwa ne kawai, gwamnatin ta ba da irin wannan tallafi ga wasu kananan hukumomin da ke da ’yan gudun hijira.