Yobe za ta tsugunar da ’yan gudun hijira 20
Kimanin ’yan gudun hijira 20 ne Gwamnatin Jihar Yobe ta zabo don sake tsugunar da su. Gwamnatin ta ce tuni ta samar musu da gidaje 20 a kauyukan Kukareta da na Bulturam-Bulin don ganin an sake tsugunar da su. Shugaban Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ta Jihar Yobe, Alhaji Goni Babagana ne ya bayyana […]
Kimanin ’yan gudun hijira 20 ne Gwamnatin Jihar Yobe ta zabo don sake tsugunar da su. Gwamnatin ta ce tuni ta samar musu da gidaje 20 a kauyukan Kukareta da na Bulturam-Bulin don ganin an sake tsugunar da su.
Shugaban Hukumar Kula da Masu Gudun Hijira ta Jihar Yobe, Alhaji Goni Babagana ne ya bayyana haka. Ya ce Hukumarsa ta ware kimanin Naira Miliyan 9 da dubu 600 wajen aiwatar da wannan muhimmin aiki. Ya ce kashi na farko ya kunshi ’yan gudun hijirar da suke da burin sake komawa gidajensu na asali ne sannan kashi na biyu kuma ya kunshi masu gudun hijira ne da suke da niyyar zama a sabon wurin da suka tsinci kansu.
Ya ce shirin zai tsugunar da masu gudun hijira ne da suka koma gidajensu na asali a garin Bulturam-Bulin da ke Damaturu da karamar Hukumar Gujba.
Ya ce hukumarsa tana shirin tallafawa karin wasu kungiyoyi 10 da su ma suke fuskantar matsalolin rayuwa kafin karshen wannan shekara.
Ya ce tuni hukumarsa ta fara aiwatar da wadansu muhimman ayyukan raya karkara kimanin 35 a kananan Hukumomin Gujba da na Gulani da yakin Bokon Haram ya shafa.