YouTube: Taska mafi tsada da hadari a Intanet
A duk wata mutum biliyan biyu da rabi ne ke ziyartar shafin.
Daga cikin shahararrun wurare da ke dauke a giragizan sadarwa ta duniya da muke kira da suna Intanet, akwai shafi ko dandalin YouTube.
Wuri ne shahararre, kuma ya kebanta da abubuwa da dama da mafiya rinjayen wurare ba su da irin siffofinsa a Intanet.
- Gwamnatin Abba za ta dora a kan ayyukan Ganduje —Kwankwaso
- NAJERIYA A YAU: Fatan Al’ummar Jihohi 5 Da Suka Canza Jam’iyyun Gwamnoninsu
Wadannan kebantattun siffofi ne suka bambanta abin da wannan dandali ke dauke da na fa’idoji da sauransu.
A wannan mako zuwa makon da ke tafe, za mu yi bayani ne a takaice kan asalin shafin Youtube da fa’idojin da ke cikin wannan shafi da kuma abubuwan da suke da matukar hadari, amma kuma suna nan su ma dauke kan wannan dandali.
YouTube daga ina kake?
Kafin samuwar wannan shafi ko kalmar YouTube a Intanet tsakanin shekarar 2000 zuwa 2004 misali, akwai shafukan yadawa da dora bidiyo irin su Daily Motion da Google Video da sauransu da a halin yanzu suka bace.
Amma shafin Google Video wanda na Kamfanin Google ne, ya ci gaba har zuwa watan Fabrairun shekarar 2005, lokacin da aka samun wani sabon dandalin dorawa da yada bidiyo a Intanet mai suna: Youtube.
Wadanda suka kirkiri wannan shafi dai wasu matasa ne su uku: Steve Chen da Chad Hurley da kuma Jawed Karim.
Ga hotonsu nan na makalo, wanda suka dauka tare da tsohon Shugaban Amurka Bill Clinton lokacin da yake Shugaban Kasa.
Ofishinsu na farko yana birnin San Bruno ne a Jihar Kalifoniya na kasar Amurka.
Bayyanar wannan shafi ko dandalin yada sakonnin bidiyo a Intanet sun kara wa fasahar Intanet shahara a duniya, saboda dandalin ya samu karbuwa sosai, kuma mutane na ziyartarsa a kowace rana da lokaci don amfanuwa da bayanan da ke cikinsa.
Cikin Oktoban shekarar 2006 Kamfanin Google ya saye wannan shafi da manhaja na YouTube daga wadannan matasa, a kan zunzurutun kudi Dala biliyan daya da miliyan 650.
Ba tsabar kudi aka ba su ba, an biya su ne da jarin Kamfanin Google a wancan lokaci.
Sai wannan ya sa su cikin sahun masu mallakar jarin Kamfanin Google su ma.
Dandalin YouTube a yau
Saye wannan shafi ko dandali na YouTube daga wadancan matasa ya sa Kamfanin Google ya jinginar da asalin shafinsa na bidiyo mai suna Google Video, ya kuma ci gaba da inganta tsari da kimtsin wannan manhaja ta YouTube har zuwa yadda take a wannan lokaci da nake wannan rubutu.
Daga cikin sauye-sauye masu tasiri akwai raba manhajar zuwa gida biyu, ta kyauta da ta kudi.
Bangaren kyauta shi ne tashar da kake cin karo da ita da zarar ka hau YouTube, shi suke kira: YouTube Free.
Na kudi kuma ita ce wadda za ka yi rajista, ka dora katinka na ATM don biyan kudin tasha a duk wata, kamar yadda ake biyan na tashoshin tauraron dan Adam irin su DSTV da Startimes.
Wannan bangare shi suke kira: Youtube Premium.
Ta bangaren nau’P’in bidiyon da ke kai an kasa manhajar ce gida biyu; bangaren sakonnin bidiyo na wasu shirye-shirye da bidiyo na wakoki na kyauta, wannan shi suke kira: YouTube Videos a sake.
Dayan kuma ya kunshi sakonnin bidiyo ne na wakoki masu hakkin mallaka (Copyrighted Music tBideos), wanda yake karkashin tsarin Youtube na kudi da bayaninsa ya gabata a sama.
Dangane da nau’o’in bidiyon da ke dandalin Youtube kuma, an kasa su zuwa bangare-bangare: akwai gajerun fina-finai da cikakkun finafinai da wakoki da bidiyo masu dauke da tarihi da bayanin abubuwa na ilimi, da sakonnin bidiyo na kan titi da wadanda jama’a ke dorawa kai tsaye don gabatar da shirye-shirye na ilimi ko bukukuwa ko karatuttuka na fadakarwa (YouTube LiVe) da sauransu.
Bayan shafin YouTube da za ka iya hawa kai-tsaye a kwamfuta ta adireshin: https://www.youtube.com, akwai manhajar Youtube ta wayar salula da za ka iya saukewa daga cibiyar manhaja da ke Play Store ko Apple Store, idan wayarka ba ta zo da ita ba.
Sannan kana iya hawa dandalin YouTube ta manhajar Youtube da ke manyan talabijin na zamani (Smart TVs).
Kana iya amfani da shafin YouTube kai-tsaye ba sai ka yi rajista ba. Idan kana son yin rajista kuma sai ka mallaki adireshin Imel na Gmail.
Wannan kadai ya isa. Ta haka ne za ka iya bude tasha (Channel) da suna na musamman, don dora naka sakonnin bidiyon kai-tsaye.
Kusan dukkan kafafen yada labaru na talabijin da jaridu da tashoshin talabijin na tauraron dan Adam da wasu cikin hukumomin gwamnati, da kamfanoni da daidaikun mutane da kungiyoyi suna da tasha a Youtube.
Kana hawa shafin za ka ci karo da nau’o’in sakonnin bidiyo birjik; ya danganci kasar da kake da harshen da kake amfani da shi a kan waya ko kwamfutarka da sabo da hawa ko sabunta zuwa, idan ba ka taba tu’ammali da shafin ba.
Kana iya tambayo irin nau’in bidiyon da kake nema kai-tsaye ta amfani da manhajar matambayi-ba-ya-bata (Search Engine) da ke sama a shafin farko.
Bayan haka, shafin YouTube na dauke ne da hanyoyin samun kudaden shiga. Daga cikin akwai dora tallace-tallace, wadanda kake cin karo da su kafin ko a tsakiyar bidiyo idan kana kallo da kudin tasha na wata-wata da masu rajista a YouTube Premium ke biya, sai kudaden da Google ke rabawa tare da masu hadin gwiwa da su wajen dora sakonnin bidiyo.
Misali, idan ka yi rajista ka bude tasha, ka samu wani adadi na mutane a tasharka, za a rika dora talla a kan bidiyon da kake dorawa.
Idan kudin ya kai Dala 100 sai a rika aiko maka a duk wata.
A karshen shekara ta 2022, Kamfanin Google ya samu Dala biliyan 29 da miliyan 320.
A karshe, shafin Youtube ne shafi mafi shahara a duniyar Intanet bayan shafin Google Search.
A shekarar 2019 misali, an kiyasta cewa a cikin duk minti guda, mutane suna dora adadin bidiyon da tsayinsa ya kai awa 500.
Sannan a duk wata maziyarta biliyan biyu da rabi ne ke ziyartar shafin, kuma a kullum ana kallon bidiyon da tsayinsa ya kai awa biliyan daya!