Yuguda ya lashe amansa, ya koma kungiyar Gwamnonin Arewa

Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya lashe aman da ya yi na ficewa daga Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa inda a ranar Talata ya bayyana komawa majalisar a wani abin da ya kira domin amfanin Arewa.Gwamna Yuguda ya fice daga Majalisar Gwamnonin Arewa ne, bayan an gudanar da zaben shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, inda Gwamnan […]

Yuguda ya lashe amansa, ya koma kungiyar Gwamnonin Arewa

Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya lashe aman da ya yi na ficewa daga Majalisar Gwamnonin Jihohin Arewa inda a ranar Talata ya bayyana komawa majalisar a wani abin da ya kira domin amfanin Arewa.
Gwamna Yuguda ya fice daga Majalisar Gwamnonin Arewa ne, bayan an gudanar da zaben shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya, inda Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amaechi ya kada takwaransa na Jihar Filato Jonah Jang da kuri’a 19 da 16.
Gwamna Yuguda ya shaida wa manema labarai a Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi cewa ya yanke shawarar komawa Majalisar Gwamnonin Arewa ne, saboda wasu fitattun dattawan Arewa sun yi masa magana inda suka ba shi shawarar ya yi hakan domin amfanin yankin.
Gwamna Yuguda wanda ya yi magana tab akin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Alhaji Yusuf Musa Gumli ya ce, “Abu ne marar dadi kan yadda siyasar Majalisar Gwamnonin Arewa a kokarinta na zaben shugaba ya kare da cece-ku-ce a tsakanin gwamnonin, kuma wani wata koma bay ace a bangarensu kan kada su ci gaba da rike wannan matsayi.”
Ya ce sakamakon haka ne iyaye daga Arewa suka kira shi suka nemi ya sauko kasa kuma ya dauki al’amura da sauki, kuma suka shawarce shi ya koma majalisar, kuma “a matsayina na da mai ladabi, na karbi shawararsu don haka na koma Majalisar Gwamnonin Arewar domin in ci gaba da kare bukatun Jihar Bauchi.”
Gwamnan ya ce ya yanke shawarar dinke barakar da ta auku, tare da mancewa da abin da ya faru a baya don komawa majalisar.
Ya ce, “Na biyu na yanke shawarar sauraren kiraye-kiraye daga dattawan Arewa, wadanda suka nemi inhadiye fushin kuma in yi kyakkyawan wakilci ga Arewa a majalisar. Kuma a matsayina na da mai biyayya na karbi kiransu na koma majalisar. Na uku ba wai na koma bangaren Jonah Jang ba ne, a’a ina aiki ne bisa umarnin Majalisar Gwamnonin Arewa ta yadda Filato za a zama cibiyar Arewa inda za a samu wakilcin da ya dace.”
Dangane da zargin yana neman tsayawa takarar Mataimakin Shugaban kasa ne a zaben shekara ta 2015, Gwamnan ya ce, ba laifi ba ne ya nemi tsayawa takarar kowane mukami na Shugaban kasa ne ko na Mataimakinsa ko kuma na Gwamnan Babban Banki, inda ya kara da cewa, “Ba laifi ba ne in tsaya takarar kowane mukami a kasar nan, matukar an bi ka’idar da doka ta tanada.”
Ya ce, “Kafin zaben, Majalisar Gwamnonin Arewa sun yanke shawarar Gwamna Shema da Yuguda su jane wa Gwamna Jang na Filato, wanda ya zama dan takarar Arewa.”
Gwamna ya ce, an sanya hadin kan Majalisar Gwamnonin Arewa a cikin hadari sakamakon faruwar lamarin, wanda ya sanya ya ji ba zai iya ci gaba da kasancewa a majalisar ba, don haka ya janye.
Ya ce, kuma a yanke shawarar ya fitar da sanarwa ga manema labarai cewa ba zai sake halartar taron majalisar ba, sai dai Sakataren Gwamnatin Jihar, kuma bai halarci taronsu na baya ba.