Yunkurin bata masu hijabi ne kawai -Limamin Wuse 2

Amfani da mata masu hijabi da masu kai hare-haren bam suka fara amfani da su, musamman a baya-bayan nan, wani sabon salo ne na bata wa musulunci suna, da kuma shirin fara musguna wa masu amfani da hijabi na hakika. Babban limamin masallacin Usman Bin Affan da ke yankin Wuse 2, Abuja, Malam AbdulJalil  Dabo […]

Yunkurin bata masu hijabi ne kawai -Limamin Wuse 2
Yunkurin bata masu hijabi ne kawai -Limamin Wuse 2

Amfani da mata masu hijabi da masu kai hare-haren bam suka fara amfani da su, musamman a baya-bayan nan, wani sabon salo ne na bata wa musulunci suna, da kuma shirin fara musguna wa masu amfani da hijabi na hakika.
Babban limamin masallacin Usman Bin Affan da ke yankin Wuse 2, Abuja, Malam AbdulJalil  Dabo Madaka ne, ya bayyana hakan a yayin da Aminiya ta nemi jin ta bakinsa a kan al’amarin.
 Malam AbdulJalil Dabo ya ce akwai shakku a kan musuluncin matan da ke wannan shigen suna kai harin, idan aka yi la’akari da maza da dama da aka kama a baya suna shiga irin ta musulunci suna kai hare-hare a coci-coci, inda ya yi misali da wanda ya taba faruwa a jihar Bayelsa, sai kuma na baya-bayan nan a Jihar Osun.
Ya bukaci jami’an tsaro da su tsaurara bincike a kan al’amarin, sannan su rika bayyana wadanda  aka Kama a yayin bincike.Ya ce duk da kasancewar musulunci shi ne addini da ya fi karbuwa a cikin hanzari a halin yanzu a duk duniya, amma addinin da kuma ma’abotansa na cike da dabaibayi ta ko’ ina, sai dai ya ce Allah Ya yi alkawarin kare addininsa.
 Ya bukaci malamai da su fadakar da jama’arsu a kan wannan sabon kalubale,  ya ce idan al’amarin ya ci gaba a haka, mata da ke sanya hijabi a bisa bin tafarkin addini  za su fuskanci tsangwama iri-iri, “ba wai zai kai ga binciken mamansu ne kawai ba, wadansu sai sun yi amfani da wannan damar sun yi masu tsirara gaba daya.’’