Yunkurin dakile canjin shekar sanatoci ba zai haifar wa PDP da mai ido ba – El-Rufa’i
Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar APC, Malam Nasir El-Rufa’i ya ce kokarin da shugabannin PDP, musamman Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Dabid Mark ke yi na dakile canjin sheka da wasu sanatoci ke shirin yi zuwa APC ba zai haifa mata da mai ido ba.A cewar, El-Rufa’i Shugaban Majalisar Dattawan bai isa ya tilasta wa sanatocin zama […]
Mataimakin Babban Sakataren Jam’iyyar APC, Malam Nasir El-Rufa’i ya ce kokarin da shugabannin PDP, musamman Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Dabid Mark ke yi na dakile canjin sheka da wasu sanatoci ke shirin yi zuwa APC ba zai haifa mata da mai ido ba.
A cewar, El-Rufa’i Shugaban Majalisar Dattawan bai isa ya tilasta wa sanatocin zama a Jam’iyyar PDP ba tare da son ransu ba.”Wannan yankuri na Dabid Mark ba zai haifar wa PDP da mai ido ba. Saboda a tsarin dimokuradiyya ba ka isa ka hana mutum canja sheka ba. Koda zancen na kotu abin da kawai muka sani shi ne wasu sanatocin ma na shirin bin sawun sauran sanatoci 11 da suka canja sheka. Insha Allah nan da zuwa karshen watan Maris sai mun canja shugabanci a Majalisar Dattawa da Wakilai. Muna fata Jam’iyyar APC za ta samu rinjaye a majalisun dokokin kasar nan,” inji shi.
Game da canjin shekar da wasu ’yan Majalisar Wakilai biyar suka yi daga APC zuwa PDP, El-Rufa’i ya ce “Yawancinsu ’yan ANPP ne da ke da matsala da gwamnoninsu. Abin da kawai muke s on jama’a su sani shi ne za a ci gaba da samun canjin sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya. Wannan shi ne siyasa kuma babu yadda za ka yi ka tilasta wa mutum yin abin da ba ya so. Akwai wadanda za a ba kudi da mukami domin su canja ra’ayinsu, amma mu ba mu da kudi ko mulki da za mu ba wani domin ya shigo APC.”
Malam Nasir ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da ya je yin rajistar zama dan APC a titin Katuru a Unguwar Sarki, Kaduna.
Ya ce tabbas akwai rikici a shugabancin APC a jihar amma suna kokari don magance matsalar wacce ya ce ba za ta gagarai magancewa ba.