Yunkurin rushe masallaci a Dutsen-Alhaji ya tada kura
kura na neman tashi kan yunkurin rushe masallacin Hudaibiyya da ke bakin kasuwar kauyen Dutsen-Alhaji da ke yankin Abuja.Aminiya ta gano tuni Musulmin da ke kauyen suka kasance cikin shirin ko-ta-kwana don su hana rushe masallacin. Mazauna kasuwar da ke kusa da masallacin sun fusata bayan sun ce mahukunta karamar Hukumar Bwari sun turo katafilolin […]
kura na neman tashi kan yunkurin rushe masallacin Hudaibiyya da ke bakin kasuwar kauyen Dutsen-Alhaji da ke yankin Abuja.
Aminiya ta gano tuni Musulmin da ke kauyen suka kasance cikin shirin ko-ta-kwana don su hana rushe masallacin.
Mazauna kasuwar da ke kusa da masallacin sun fusata bayan sun ce mahukunta karamar Hukumar Bwari sun turo katafilolin da suka yi rusau a wani bangare na kasuwar a ranar Alhamis din makon jiya, don rusa masallacin.
A ranar Talata da misalin karfe 6:00 na safe ne mazauna kusa da masallacin suka ja daga don hana rushe masallacin.
Shugaban masallacin Alhaji Ibrahim Shu’aibu ya ce an yi rushe-rushe a kasuwar, kuma a nan masallacin yake, sai dai ya roki gwamnati ta samar da wani wuri kafin ta kai ga rushe masallacin idan ta tsara cewa masallacin yana daya daga cikin wuraren da za a rushe.
Ya bukaci hukumomi su yi abin da ya dace, idan ba haka ba za su dauki matakan da suka dace.
“Hukumar Tsara Birnin Abuja ko karamar Hukumar Bwari ba ta ba mu takardar cewa mun gina masallacin ba bisa ka’ida ba, don haka muna kira ga hukumomi da kuma ’yan kasa su fahimci muhimmancin kare duk wani mutum da ke zaune a kauyen,” inji shi.
Ya ce, koda an gina masallacin ba bisa ka’ida ba, ya kamata a ba su wa’adi ba wai rana tsaka a zo a ce za a rushe masallacin ba.
Mai magana da yawun Hukumar Tsara Birnin Tarayya, Kalu Emelu ya ce ba shi da masaniyar yunkurin rushe masallaci a kauyen Dutsen-Alhaji.