Yunkurin sace akwatin zabe ya yi sanadin mutuwar mutum daya a Ibadan

Yunkurin sace akwatin zabe da wadansu ’yan bangar siyasa suka yi a wata rumfar zabe a Ibadan a ranar Asabar ya yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Monsuru Hamzat, wanda ya gamu da ajalinsa a dalilin harbin bindiga da ’yan bangar suka yi. Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga ’yan jarida, Kwamishinan ’Yan […]

Yunkurin sace akwatin zabe ya yi sanadin mutuwar mutum daya a Ibadan

Uwargidan Gwamnan Jihar Oyo Florence Ajimobi tana kaxa quri’arta a ranar Asabar a Ibadan

Yunkurin sace akwatin zabe da wadansu ’yan bangar siyasa suka yi a wata rumfar zabe a Ibadan a ranar Asabar ya yi sanadin mutuwar wani matashi mai suna Monsuru Hamzat, wanda ya gamu da ajalinsa a dalilin harbin bindiga da ’yan bangar suka yi.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin ga ’yan jarida, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olokulu ya ce ’yan bangar suna cikin tawagar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Ambasada Taofeek Arapaja ne wanda ya ziyarci rumfar zabe ta 2 a yankin Agbongbon a birnin Ibadan, inda dogarawansa suka rika harbi da bindiga a daidai lokacin da ake kidayar kuri’u, bayan kammala zabe. Ya ce daya daga cikin harsashin bindigar ne ya samu matashin, inda ya yi sanadin mutuwarsa a asibiti.

Kwamishinan ’Yan sandan ya ce jim kadan bayan aukuwar lamarin sai tsohon Mataimakin Gwamnan da tawagarsa da suka hada da dogarawansa biyu masu suna Akin da Edilla da sauran yaransu suka bace. Ya ce ya mika wannan al’amari ga Sashen Binciken Manyan Laiffuka (SCID) da ke Iyaganku  Ibadan, domin ci gaba da bincike.

Da yake kare kansa, Ambasada Taofeek Arapaja ya musanta cewa yana da hannu wajen aukuwar lamarin. Ya ce, an yi nufin hallaka shi ne maimakon matashin. “Ban taba ganin irin wannan a baya ba, domin an yi nufin hallaka ni ne lokacin da na ziyarci rumfar zaben,” inji shi. Ya ce a baya ya saba kada kuri’arsa a rumfar zabe ta Agbongbon ne wanda ya yi hakan a wannan rana bayan mutane sun kammala kada kuri’a da aka fara kidayawa.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa wata kungiyar ’yan daba mai suna ‘One Million Boys’ da ta yi kaurin suna wajen aikata miyagun ayyuka a birnin Ibadan ce ta yi wa rumfar zaben dirar mikiya, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi lokacin da suka fahimci an cire allon hoton ubangidansu an maye gurbinsa da hotunan wadansu ’yan takara na daban.

’Yan sanda sun hanzarta kai dauki inda suka fatattaki ’yan dabar daga wurin.

An tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na birnin Ibadan da sauran garuruwan jihar a lokacin da ake gudanar da zaben na ranar Asabar.

Jama’a cikin shauki sun fito kwai da kwarkwata sun kada kuri’u don zabar mutanen da suke so su shugabance su a ranar.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta