Yunkurin samar da zaman lafiya a Jihar Zamfara
Mai yiwuwa idan komai ya tafi yadda masu kula da tsaron Jihar Zamfara suka tsara kuma suke fata ya tabbata, mai karatu zuwa lokacin da kake karanta wannan mukala da yawa daga cikin ’yan ta’addan da yau kusan shekara goma suka addabi jihar da sace-sacen dabbobi da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da […]
Mai yiwuwa idan komai ya tafi yadda masu kula da tsaron Jihar Zamfara suka tsara kuma suke fata ya tabbata, mai karatu zuwa lokacin da kake karanta wannan mukala da yawa daga cikin ’yan ta’addan da yau kusan shekara goma suka addabi jihar da sace-sacen dabbobi da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sauran miyagun ayyukan ta’addaci na kona dukiyoyin al’umma da mayar da dubban jama’ar jihar ’yan gudun hijira, sun fara mika makamansu da niyyar sun tuba sun daina aikata ayyukan ta’addanci haihata-haihata.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar kuma Shugaban Kwamitin Samar da Zaman Lafiya da Sasantawa na Jihar, Alhaji Usman Nagogo da Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Mohammed Bello Matawalle ya kafa bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayun da ya gabata, shi aka ji yana fadin haka a karshen makon jiya ga manema labarai a Gusau. Ya ba da tabbacin cewa a cikin wannan makon ake sa ran ’yan ta’addan za su fara mika makamansu ga mahukunta, niyyar da ya ce tuni wani dan ta’addan ya mika bindigoginsa biyu ga Shugaban Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah na Kasa baki daya Alhaji Muhammadu Kiruwa .
Samuwar haka ya biyo bayan irin dukufar da Kwamishinan ’Yan sandan da sauran jami’an tsaro a jihar suka yi wajen tattaunawa da shugabannin ’yan ta’addan da kuma ’yan sa-kai (farar hula masu yaki da ’yan ta’addan) da sauran masu ruwa-da- tsaki.
Kamar yadda Kwamishinan ’Yan sandan ya fada, mika makaman ya biyo bayan tattaunawar da kwamitinsa ya dukufa a kai da kuma ’yan kungiyoyin sa- kai.
Da farko an yi zama daban-daban daga bisani kuma aka yi zaman gaba-da-gaba da wakilan ’yan ta’addan da na kungiyoyin sa- kai a kan sa idanu da sauraren Gwamnan Jihar. Hakan inji shi, shi ya fara wanzar da ’yan kungiyar sa-kan a fadar Mai martaba Sarkin Dansadau Alhaji Hussaini Umar suka mika Fulani 25 da suka hada da maza da mata da kananan yara. Su ma ’yan ta’addan kashegari suka mika wa jami’an tsaro mutum 15 da suka yi garkuwa da su.
Rahotanni daga jihar a wancan mako sun tabbatar da cewa, ana ta samun sako wadanda bangarorin biyu suka yi garkuwa da su ko suka kama, har ma akwai wadanda suka shafe wata bakwai suna tsare wadanda a karshe aka mika su ga Gwamnan Jihar.
Maganar da ake yi yanzu an fara samun walwalar cin manyan kasuwannin jihar irin su Kasuwar Daji da ta Mada da ta Dangulbi da ta Dansadau da ta ’Yar-tasha da sauransu, sabanin wasu shekaru da dama an daina maganar cinsu, saboda tabarbarewar tsaro. Hakazalika Fulani da cin kasuwannin ya faskara gare su, yanzu suna zuwa cin kasuwannin, sabanin a baya da ’yan kungiyar sa-kai, ke kashe su duk inda suka gansu, kashe-kashen da kan harzuka ’yan ta’addar da suke cikin dazuzzukan jihar kara kai hare-hare ga garuruwa da kauyukan jihar a matsayin ramuwar-gayya.
Babbar hanyar nan da ta hada Jihar Zamfara da Jihar Katsina wato ta Jibiya zuwa Kolomi, zuwa yanzu an yi nasarar bude ta, abin da ke kara nunin cewa sannu a hankali ana kara samun ingantuwar tsaro a jihar da makwabciyar ta Katsina da ita ma take fama da makamanciyar annobar ta Jihar Zamfara.
Babban aikin da ke gaban mahukuntar jihar kamar yadda Kwamishinan ’Yan sanda Alhaji Nagogo ya fada, shi ne yadda ’yan ta’addan za su mika makamansu tsakani da Allah, al’amarin da zai tabbatar wa duniya da mutanen kasar nan musamman na jihar cewa ta’addancin ya kawo karshe, inda samuwar hakan ka iya rage aikata ta’addancin a wasu jihohi.
A bisa ga al’ada, duk lokacin da aka zo batun tattauna irin wannan da za ta kawo karshen ta’addanci, wadanda al’amarin ya shafa sukan gitta wa juna wasu sharudda da akasari aka fi samu daga bangaren jama’a a kan mahukunta.
Alal misali a 2015, da gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari ta samu yin yarjejeniya da ’yan ta’adda masu satar shanu a wasu sassan jihar, ’yan ta’addan sun nemi a samar musu da abubuwan more rayuwa irin su hanyoyi da makarantun boko da ruwan sha a yankunansu. ’Yan ta’addan a lokacin an ce sun kai 300, wadanda suka mika makamansu da suka hada da bindiga kirar AK-47, har 104 da wasu bindigogi 267.
A Jihar Zamfara rahotanni sun tabbatar wani rikakken mai satar shanu da garkuwa da mutane a yankin Tsafe da Mada mai suna Ado Aleiro da mahukunta suka nema don yin sulhu a cikin wani daji da ke kauyen Munhaye, cewa ya yi lallai sai an biya shi diyyar shanunsa 400 da suka salwanta a cikin rikice-rikicen, sannan a sake gina masa gidansa da ’yan kungiyar sa- kai suka kona, bukata ta karshe kuma sai mahukunta sun fitar da burtaloli da kuma samar wa makiyaya wuraren kiwo.
Ko shakka babu kamar yadda Ado Aleiro ya nemi biyan wadancan bukatu daga mahukuntar Jihar Zamfara da yawa daga cikin Fulani makiyaya da ake zargi da ta’addanci za su nemi tasu biyan bukatar daga gwamnatin jihar. Idan dai ba bukatar al’umma suka nema ba kamar ta samar masu kayayyakin more rayuwa da gina musu rugage a sassan jihar, to, bai kamata mahukuntan su saurare su ba. Ko ba komai ai sun aikata miyagun laifuffuka na kashe daruruwan mutanen da ba su-ji-ba su-gani-ba, baya ga miliyoyin nairorin da suka karba a matsayin kudin fansa daga iyalan wadanda suka yi garkuwa da su. Kamata ya yi a tsaya a kan tsarin ba-kare-bin-damo. Amma wani hanzari ba gudu ba, lallai gwamnati ta himmatu wajen samar da ayyukan more rayuwa ga yankunan irin wadancan mutane. Hakazalika ta yi kokarin fitar da burtaloli da rugage a duk inda ake bukatarsu a cikin jihar.
A nan akwai bukatar shigowar Gwamnatin Tarayya yadda ya kamata.
Daga karshe ina taya Gwamna Bello Matawalle da Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Usman Nagogo da jami’an tsaro da sauran masu ruwa-da-tsaki, murna kan jajircewarsu wajen ganin an kawo karshen wadannan mummunan ayyuka na ta’addanci da suke kawo koma baya ga rayuwar al’umma a fannonin tattalin arziki da zamantakewa baki daya. Idan har an yi nasara kawo karshen wannan annoba, to, ko ba komai Gwamnan Jihar Zamfara Matawalle yana da abin bugun kirji ya ce ya yi a cikin kwana 100, na hawansa mulkin. Sauran gwamnonin jihohi da ake fama da irin wadannan annoba kalubalenku!