Yunkurin tsige Buhari babban abin takaici ne – Shugaban APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana yunkurin da wasu ‘yan majalisa ke yi na tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin abin takaici.  Shugaban Jam’iyyar ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust TV a Abuja a ranar Talata.  Yin ’yar […]

Yunkurin tsige Buhari babban abin takaici ne – Shugaban APC

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya bayyana yunkurin da wasu ‘yan majalisa ke yi na tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a matsayin abin takaici. 

Shugaban Jam’iyyar ya yi wannan furuci ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Trust TV a Abuja a ranar Talata.

Abdullahi Adamu, wanda tsohon dan Majalisar Dattijai ne, ya ci gaba da cewa wannan yunkuri da ‘yan majalisar ke kokarin yi a bisa furucinsu, abin Allah-wadai ne, kuma sun sauka daga kan tsarin da ya dace.

“Tsige shugaba kan karagar mulki ba birgewa ba ne, illa takaici, [kuma] an daina yayinsa.

“Kodayake da irin wannan majalisar ta kasa, babu mamaki idan sun yi [wannan yukuri]. Hakan na faruwa ne a kowanne mulki na dimukuradiya, amma wadanda suka soma, tuni suka daina,” inji Shugaban na APC.

A kwanan baya ne wasu ‘yan Majalisar Dattawa daga jam’iyyar PDP suka yi barazanar tsige Shugaba Buhari idan ya gaza magance matsalar tsaron da ake fama da ita a Najeriya a cikin wa’adin makwanni shida.

‘Yan Majalisar sun yi wannan ikirari ne a wani taron ‘yan jarida kafin majalisar ta tafi hutun wata biyu.