Yunkurin tsige Shugaba Jonathan ya kankama
Yunkurin tsige Shugaban Goodluck Jonathan ya kankama, inda aka samu ’yan majalisar dattawa 20, da kuma ’yan majalisar wakilai a kalla mutum200. wadanda suka rattaba hannu kan yunkurin. Wannan yunkurin dai ya biyo bayan takun sakar da Shugaban majalisar wakilai Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya shiga da jami’an ’yan sanda, wadanda suka mamaye majalisar, har […]
Yunkurin tsige Shugaban Goodluck Jonathan ya kankama, inda aka samu ’yan majalisar dattawa 20, da kuma ’yan majalisar wakilai a kalla mutum200. wadanda suka rattaba hannu kan yunkurin. Wannan yunkurin dai ya biyo bayan takun sakar da Shugaban majalisar wakilai Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya shiga da jami’an ’yan sanda, wadanda suka mamaye majalisar, har ta kai ga ya sha barkonon tsohuwa shi da tawagarsa, inda aka yi yunkurin hana su shiga cikin majalisar..
A makon da ya gabata ne ’yan majalisar wakilai suka bijiro da yunkurin tsige Jonathan, inda aka fara tattara sa hannun wadanda suka amince da yunkurin, har ta kai ga sun samu amincewar a kalla mutum 200, kamar yadda Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Mista Samson Oasagie ya bayyana wamanema labarai a Abuja.
Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa, ’yan majalisar dattawan sun yi matukar nuna takaicinsu kan yadda jami’an tsaro suka kai wa majalisar farmaki, har ma suka harba wa Shugaban Majalisar Alhaji Aminu Waziri Tambuwal barkonon tsohuwa.
A cewar danmajalisar dattawan da ya gana da manema labarai, “fiye da mutum 20 a cikinmu sun rattaba hannu kan takardar yunkurin tsige shugaban, a daidai lokacin da muka kusa samun kashi 2/3.”
Aminiya ta samu labarin cewa, danmajalisar dattawan da yake tattara sa hannun wadanda suka amince da yunkurin tsige shugaban kasa,ya fito ne daga yankin Kudu maso Yamma.
“A shirye muke mu kai ga kowane irin matsayi, saboda ba za mu bar al’amura su ci gaba da kasance a haka ba,” inji shi.
Bisa la’akari da tanade-tanaden Kundin tsarin mulki na shekarar 1999, akwai bukatar dole sai 1/3 na sanatocin sun sanya hannu kafin a tsige shugaban kasar.
A halin yanzu dai akwai bukatar akalla ’yan majalisar dattawa 36 daga cikin 109 su gabatar da wannan bukata a gaban majalisar, kamar yadda wakilinmu ya tattara bayanai.