Yunusa Yellow: Duniya ina zaki da mu?
Na dade ina tuno Yunusa Yellow tare da tunanin ko a wane irin hali yake a Jihar Bayelsa tun bayan da Gwamnatin Kano ta mika shi. Abin da ya fi kai kawo a cikin raina shi ne wane irin hukunci aka yanke masa? Sannan ko akwai masu bin kadinsa?Nasan akwai mutane da dama da ke […]
Na dade ina tuno Yunusa Yellow tare da tunanin ko a wane irin hali yake a Jihar Bayelsa tun bayan da Gwamnatin Kano ta mika shi. Abin da ya fi kai kawo a cikin raina shi ne wane irin hukunci aka yanke masa? Sannan ko akwai masu bin kadinsa?
Nasan akwai mutane da dama da ke da labarinsa a kwanakin baya, shi ne mutumin da wata Kirista ta Muslunta saboda so da kaunar da take yi masa, har ta kai ga ya aureta daga bisani, kuma sai abin ya baci inda ‘yan uwanta ke ganin kamar tursasata ya yi wajen karban Muslunci, har ta kai ga ana yi masa kallon mutumin da kawai zaman lalata yake da ita. Da rigima ta ki ci, ta ki cinyewa sai Gwamnatin Kano ta kama shi ta mikashi ga mahukuntar Jihar da yarinyar ta fito. Bayan da aka mika musu shi har yanzu ni dai ban sake jin wani labarin sa ba, hatta, masu rubuce-rubuce a kansa a kafar facebook sun daina, amma ban sani ba ko an sake shi, wanda kuma hakan da wuya, musamman idan na tuno da wani hotonsa hannusa sanye da ankwa sai na ji a raina da kamar wuya a ce sun sake shi. Ko ma dai mene ne Allah na tare da kai Yunusa Yalo.
Haka nan na kan tuno wani bawan Allah da aka kama shi ake tuhumarsa da kashe wata mata Kirista da ta yi batanci ga fiyayyen halitta Annabinmu Muhammadu (S.A.W) a kofar Wambai Kano da kuma wanda ya mika kansa ya ce shine ya yi kisan. Har yanzu babu wani takamaiman bayani kan ko a wane hali suke. Muna fatan duk Allah ya kubutar da su.
Nasiru kainuwa Hadejia 08100229688 [email protected]