Yunwa a ba ki a huta
Fatara dai mummunar aba ce da kowa ke neman tsari daga gare ta. Amma idan har fatara ta yi wa dan Adam kanta, yakan gamu da batan basira, kuma yana iya yin komai cikin hanzari don tsira daga sharrinta. daya daga cikin illolin fatara ita ne haddasa lalacin da kan janyo yunwa da cututtuka da […]
Fatara dai mummunar aba ce da kowa ke neman tsari daga gare ta. Amma idan har fatara ta yi wa dan Adam kanta, yakan gamu da batan basira, kuma yana iya yin komai cikin hanzari don tsira daga sharrinta. daya daga cikin illolin fatara ita ne haddasa lalacin da kan janyo yunwa da cututtuka da kuma rashin taimakon kai-da-kai. Wanda duk ya tsinci kansa a cikin irin wanan halin zai yi ta kokarin ganin ya samu mafita cikin sauki, kuma da gaggawa. Sau da yawa sai ka ji abubuwan da irin wadanda fatara ta addabesu ke aikatawa suna da ban mamaki matuka da kuma ban haushi da takaici, cike da wauta da sakarci.
Irin haka ne ta kai wani magidanci, mai suna Malam Yusuf Bala, yin dabarar-rashin-dabara don samun abin ciyar da iyalinsa da suka kai gargara, suna kwankwance shajaran-majaran saboda tsabar yunwar da ta kwantar da su. Malam Yusuf ya yi cinikin buhun shinkafa a Kwanar Singa da ke Unguwar Fagge-ta-Gabas a Jihar kano, kuma bayan an sallama masa, sai ya ce zai je ya kawo kudi, amma ga wani dansa nan, dan shekaru biyar zai jira shi a wurin kafin ya komo da su.
Bayan Malam Yusuf Bala ya saba buhun shinkafa, ya tafi abinsa, sai Maishagon, Alhaji Suleiman Bagudu ya ga uban yaron bai komo ba, ga shi kuma lokacin tashi daga kasuwa ya yi, bai san yadda zai yi da yaron ba, sai ya ce da yaron ya kai shi gidansu don ya karbo kudin shinkafarsa da kansa. Haka nan dai Alhaji Suleiman Bagudu ya tasa keyar yaron, tinkis-tinkis har zuwa Unguwar koki, a yankin karamar hukumar Dala a cikin Birnin Kano. Amma saboda ladifiyar hujjar da Malam Yusufu Bala ya bayar ta rashin kudi da ya ta hana shi komowa don tahowa gida da yaronsa, da kuma tsananin bukatar wannan shinkafar don kyautata wa iyalansa, sai Alhaji Suleiman Bagudu ya tausaya masa, ya kuma ce ya yafe masa kudin buhun shinkafar da ya kasa biya, ya kuma taimaka masa da wasu ’yan kudi don yin cefane.
Wannan kissar ta Malam Yusufu Bala mai tayar da hankali ce domin ta nuna yadda halin matsin da jama’a ke ciki wanda ke kai su ga karya billensu ko zubar da mutuncinsu don neman rufin asiri, sa’annan kuma tausayawar da Alhaji Suleiman Bagudu ya yi abar yabawa ce, domin hakan ya nuna cewa na Annabi dai ba su karewa. Haka nan kuma a wasu ’yan makwannin da suka gabata wani abin al’ajabi da ya jibanci tsabar fatara da halin matsi sun haddasa yunwar da ta ingiza wani malamin makaranta, a garin Igede Ekiti da ke yankin karamar Hukumar Iredopun/Ifelodun ta Jihar Ekiti, haura garun makwabciyarsa, ya kuma sace mata tukunyar amalar da ta tuka.
Jaridun yankin Kudu-maso-Yammacin kasar nan sun ruwaito rahoto daga Unguwar Ogodege game da wannan malamin makaranta da ke koyarwa a Baptist High School, wanda sai bayan da wata makwabciyarsa ta kammala tuka amalar da za ta yi kalaci da ita, ya hauro garu, ya yi awon gaba da tukunyar, bayan matar ta fice daga kicin don dauko kwanon da za ta zuba, ta kai daki, don ta ci a tsanake. Bayan mata mai amala ta komo da kwano, sai tukunyar amalar ta ce dauke-ni-inda-kika-ajiye, saboda haka nan sai ta buga ihun da ya janyo hankulan sauran makwabtan da suka firfito da kulake , domin sun ji tana ta kururuwar barawo. Sai daga bisani aka fahimci cewa ashe malamin makarantar da ke makwabtaka da ita ne barawon, bayan ta gan shi yana cin amalan da manja, tare da wasu ‘ya’yansa guda biyu.
Wannan abu ya bai wa matar da ke da amalar mamaki da tausayi, saboda haka nan sai ta koma gidanta, ta debo miya mai rai da lafiya, ta ba su don su ji dadin cin amalar har su koshi. To amma sai dai tsananin wuya ko wahalar da za ta iya ta kai malamin makaranta satar tukunyar amala a Jihar Ekiti da kuma uban wancan yaron na Jihar Kano, wadanda matsi da rashi suka kai shi jinginar da dansa kan buhun shinkafa, ba kwararan hujjoji ne da za su dogara da su don aikata abubuwan da suka sanya aka ga wallensu ba. To amma an ce fatara ba hauka ba ce, ba kuma za ta sanya mutum ya kauce hanya, ya aikata masha’a ba. Idan da kwadayi da za a gamu a wulakanci, idan kuwa mutum ya jure, shi ke nan ya huta. Mutunci dai madarar ne, idan kuma ya zube bai kwasuwa. Da dai wadancan mutanen sun daure, sun amince cewa wuya ba ta kisa, ai da yanzu sunayensu ko kissoshinsu ba su yadu a duniya, kowa ya ji ba.
Abin takaici ne a wannan kasa, a halin yanzu, da aka shiga wani irin hali na rashin abinci da ke sa wasu mutane yin abubuwa masu ban tausayi da kuma ban haushi. An dai san cewa abinci yana da muhimmanci ga rayuwar dan Adam, amma ba sai mutum ya yi abin da za a kyare shi, ko a tsangwame shi ba, kafin ya samu abin da zai kai bakin salati, domin an ce gari da mutane ai maye ba zai ci kansa ba. Kowane irin halin kunci mutum ya shiga zai gamu da sauki, domin Allah zai kawo masa masu taimakawa. Hakuri dai shi ne maganin zaman duniya, kuma idan aka ga ba a samu alfanu ba game da shi, to kadan aka yi.
Ya kamata mahukunta su tuna fa cewa hakkin rayuwar talakawansu da kuma walwala da jin dadinsu sun dogara ne kacokan a wuyansu, kuma kamata ya yi su dinga tabbatar da yanayi da halin da jama’arsu ke ciki a kodayaushe don gano masu tsananin bukata wacce rashinta kan iya kai su ga tagayyara ko aikata wani abin da ba shi ke nan ba. Fatara da talauci dai sun samu gindin zama a kasar nan, jama’a kuma na fama da rashi da matsi wadanda kan haddasa tsananin yunwa da mayata. Dangane da haka ne ake kira ga masu hannu-da-shuni da kuma hukumomi su taimaka wajen saukaka wa wadanda ke fama da tsananin rashi, ko kuma su taimaka musu ficewa daga cikin kangin bukatar da za ta jefa su cikin halin kaka-ni-ka-yi, Ita dai yunwa wahalarwa ke gare ta, maganinta kawai a ba ta don a huta da azabarta.