Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah
Kukah, ya ce gwamnati ta gaza kawo ƙarshen yunwa a Najeriya.
Bishop Matthew Hassan Kukah na Cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato, ya ɗora alhakin turmutsitsin da ys auku a Abuja, Oyo, da Anambra kan gazawar gwamnati wajen magance yunwa da fatara a Najeriya.
Ya bayyana haka ne yayin isar da saƙon Kirsimeti, inda ya ce duk da samun ‘yancin kai sama da shekaru 60, Najeriya har yanzu tana fama da cin hanci, bambancin ƙabilanci, da rashin ci gaba mai ma’ana.
- Najeriya ba ta cikin ƙasashen da suka fi cin bashi a Afirka – IMF
- Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Babiana
“Turereniyar da ta faru a wuraren rabon abinci a Okija, Ibadan, da Abuja abun takaici ne kuma shaida ce ta irin yanayin ƙunci da ake ciki,” in ji Bishop Kukah.
“Gazawar gwamnati wajen magance yunwa a rayuwar jama’a ya sanya rabon abinci ke sa ana mutuwa.”
Ya kuma soki yadda ake daƙile matasa wajen shiga siyasa, musamman ta hanyar sanya kuɗi mai tsada wajen sayen fom ɗin takara.
“Akwai dokar da ta bai wa matasa damar yin takara, amma har yanzu rashin dimokuraɗiyya da matsalolin kuɗi suna zame wa matasan cikas,” in ji shi.
Duk da ya yaba da shirin lamunin karatu na gwamnati, Bishop Kukah ya nemi a faɗaɗa shirin ta hanyar koyar da matasa sana’o’i da ilimin fasaha.
Ya kuma yi kira da a samar da tsari mai kyau don magance matsalar rashin tsaro.
“Rashin tsaro ya samo asali ne daga cin hanci. Ba za mu iya magance matsalar ba sai mun magance waɗannan matsalolin,” a cewarsa.
Bishop Kukah, ya yi kira ga gwamnati da ta yi aiki tare da ƙungiyoyin da ke tallafa wa marasa galihu kamar coci da sauransu.
“Waɗannan abubuwan na iya kaucewa. Gwamnati tana da alhakin inganta rayuwar duk wani ɗan ƙasa,” in ji shi.