Yunwa da kishirwar banza ko na alheri?

Ya ku Gizagawan Zumunci, idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, za mu shiga cikin bakon wata. Wata mai alfarma da adimbin albarka. Watan da wasu za su dandani yunwa da kishirya mai albarka kuma mai alheri; a yayin da wasu za su sha bakar yunwa da tsananin kishirwa, amma na banza.“Ta yaya mutum […]

Yunwa da kishirwar banza ko na alheri?
Yunwa da kishirwar banza ko na alheri?

Ya ku Gizagawan Zumunci, idan Allah Ya kai mu mako mai zuwa, za mu shiga cikin bakon wata. Wata mai alfarma da adimbin albarka. Watan da wasu za su dandani yunwa da kishirya mai albarka kuma mai alheri; a yayin da wasu za su sha bakar yunwa da tsananin kishirwa, amma na banza.
“Ta yaya mutum zai sha yunwa da kishirwa da sunan ibadar azumi, amma kuma ya tashi a banza? Kana nufin ba zai samu ladar da ake samu ba?” Na san wasu za su yi wannan tambayar, don haka bari in sake jaddada abin da na fada a baya. kwarai kuwa, ka fadi da babbar murya, tabbas wasu ba za su samu wani amfani ko wata lada ba daga azuminsu. Za su tashi a fankan-fayau, za su gama shan yunwa da kishirwa a banza. Wasu kuwa babu shakka za su girbi alheri a sakamakon azuminsu, a sakamakon yunwarsu da kishirwarsu.
A wannan  wata da muke dakon zuwansa makon gobe, duk wanda ya azumce shi bisa kyakkyawan aiki, ta hanyar bin ka’idojin azumi, kamar yadda Allah Ya shar’anta, shi ne zai samu lada mai kima, zai girbi alheri mai danko. Irin wannan mutum, shi ne wanda ya tsaya kai da fata wajen kare hakkokin azumi, wanda ya tsare ibada yadda ya kamata, ya hana kansa aikata dukkan wasu ayyukan assha, ayyukan sabo, ayyukan da Allah Ya hana shi aikatawa. Mutumin da ya kyautata dangantakarsa da al’umma, wanda ya kyautata dabi’unsa, ya kyautata wa iyaye da ’yan uwansa na jini da makwabta da sauran al’umma. Duk mutumin da ya kyautata aikinsa da sana’arsa bisa koyarwar Manzon Tsira a cikin wannan wata da bayansa, shi ne zai dace da cin gajiyar yunwarsa da kishirwarsa. Duk mutumin da ya kare kansa daga cuta ko zaluntar dan uwansa a wannan wata, duk wanda ya kyautata wa iyalinsa a cikin wannan wata mai alfarma, shi ne za a yi wa san barka, domin kuwa zai dace da dukkan albarkokin da ke cikin watan Ramadan.
A hannu daya kuwa, kamar yadda na ambata a baya, akwai wadanda za su sha yunwa da kishirwar banza. Irin wadannan mutane, su ne masu kunnen kashi, wadanda suka kasa bin ka’ida da shari’ar azumi. Su ne za ka ga suna azumi, amma azuminsu bai hana su cutar al’umma ba. Idan ’yan kasuwa ne, irinsu ne za ka ga suna kara tsawwala farashin muhimman kayan bukatar al’umma. Irinsu ne za ka ji suna gulma suna giba suna la’antar bayin Allah. Irin wadannan mutane da za su zama asararru a cikin wannan wata, su ne za su kasance tare da shaidan, domin kuwa ba za su yi wani yunkuri na kyautata wa al’umma ba.
Duk da suna dauke da azumi, irin wadannan karkatattun mutane, su ne za su kasabnce cikin sabon Allah da fajirci. Iyakar azuminsu zai kasance daga asuba ne zuwa magariba, daga nan kuma za su fantsama cikin aikata laifuka. Su ne zinace-zinace, su ne shan giya da sauran ayyukan tantiranci. Babu shakka, irin wadannan mutane, su ne za su kasance masu yunwa da kishiryar banza, domin kuwa babu albarka a cikin azuminsu.
Ya ku Gizagawa da sauran al’ummar Allah da Annabi, ga wata ’yar shawara nan daga dan uwanku: Mu kasance masu bin kadin gaskiya da adalci. Mu kasance tsarkaka, masu aiwatar da ibadar azumi cikin bin ka’idojin da addininmu ya tanadar. Mu kasance masu kyautata ayyukanmu da sana’o’inmu, mu yi adalci, mu nemi albarka ba yawan riba ba. Mu tausaya wa junanmu domin mu dace da rahamar Allah. Mu kyautata wa iyayenmu da ’yan uwanmu na nesa da na kusa, mu yada kauna da ziyartar juna. Mu yawaita ayyukan alheri a cikin wannan wata.
Fatarmu ita ce, mu dace da albarkar da ke kunshe a cikin wannan Mashahurin Wata – Ramadan Karim! Allah Ya sa mu dace, Ya ba mu ikon shiga cikin watan lafiya, Ya ba mu dacewa da aiwatar da dukkan ibadoji a cikinsa bisa dacewa da sunnar Manzon Tsira, Muhammadu (SAW). Allah Ya sanya mu kasance ’yantattun bayi a ciki da bayan Ramadan Karim. Amin-summa-amin!
***
A yayin da muke niyyar shiga watan albarka, Sanusi Skipper Kura 08035946169, sako ya aiko ga Gizagawa da dukkan al’umma cewa: “Gizago, fatan alheri gare ka da addu’a tagari. Ina mai addu’ar fara azumi lafiya da kare shi lafiya ga dukkan Musulmin duniya.”
***
Shi kuwa Hussaini Muhammad Binanchi da Isa Kwafsi (Ba Ka Soyayya) 08087436699, sakon hadin giwwa suka aiko, suna cewa: “A makon da ya gabata ne Shugaban Hukumar Zabe Ta kasa ya fidda sanarwar cewa, duk dan Najeriya ya sha kuruminsa kawai, domin kuwa za su inganta zabe mai zuwa in Mai Sama Ya kai mu. To, Baturen zabe, Allah Ya ba ka ikon yin hakan amma ka sani, an fa dade ana ruwa kasa na shanyewa, ko ba haka ba?”
***
Shi kuwa Aliyu Sani Tsafe, Jihar Zamfara 07036954174, koke ya aiko, yna cewa: “Ya kai Gizago da sauran ma’aikatan Aminiya mai farin jinni, mai albarka; muna kara gode maku game da taimaka wa al’umma wajen fayyace gaskiya game da aikinku, tare da tausaya wa jama’a idan aka cuce su. Saboda haka, muna kara neman taimako da a kara isar mana da kokenmu, ko Allah Ya sa a dace.
“Mu ne jama’ar da ke aiki a karkashin Hukumar Sadarwa ta Najeriya (Rural Telephone) da ke Jihar Zamfara, muka kwashe wata 52 babu albashi, ga iyalai da kuma rashin abin yau da kullum, ga azumi na gabatowa; wayyo Allah! Ya kamata a taimaka wa rayuwar bil-Adama. Don Allah, duk wani mai hali da zai iya taimaka mana a fitar mana da hakkinmu, ya y haka, domin shi ma Allah zai taimake shi a gobe kiyama.”
***
 A labarin farin ciki kuwa, na samu sako daga daya daga cikin iyayen Gizagawan Jihar Nasarawa, Alhaji Abdullahi Zakari, Zanwan Lafiya 08096430960; yana cewa: “Assalamu alaikum. Alhamdu lillahi. Ina mai matukar farin cikin sanar da kai cewa, Allah Ya ba ni haihuwar da namiji ranar 29-06-2013, wanda za a yi suna gobe Asabar idan Allah Ya kai mu. Za a rada sunan ne a babban zauren kofar Zanwan Lafiya, da karfe 7:30 na safe ga wanda Allah Ya ba ikon zuwa.”
Shi ma Mataimakin Shugaban Gizagawan Abuja Lawal Abuja, Lawal Ahmad 08069551084, ya samu karuwar haihuwar jariri a Lahadin da ta gabata.
Muna taya Zanwan Lafiya da Lawal murna da addu’ar Allah Ya raya, Ya dayyaba zuri’a. Allah Ya albarkaci dukkan ’ya’yanmu da zuri’armu gaba daya, amin. – Gizago.
***
Shi kuwa Bagizage Buhari Yunusa 08063330403, za a daura masa aure ne a yau Juma’a, wanda za a gabatar a masallacin Juma’a na Maraba da karfe 2:00 na rana.
Allah sa albarka, amin. – Gizago.