Yunwa: Jama’a sun daka wa motar Dangote wawa a Katsina
Mata da maza da kananan yara suna daukar buhunan kayan abinci suna awon gaba da su daga babbar motar
Jama’ar gari a Jihar Katsina sun daka wa wata motar kamfanin Dangote wawa, inda suka yi awon gaba da kayan abincin da take dauke da su.
Hakan ta faru ne a yayin da matsin rayuwa da tsadar kayan masarufi a Najeriya suka kai makura, inda kudin buhun masara ya kusa ninka mafi karancin albashi.
A bidiyon wasoson da ke yawo a kafofin sada zumunta, an ga maza da mata da kananan yara suna daukar buhunan kayan abinci suna awon gaba da su daga babbar motar da ke kan babbar hanya.
Wasu daga cikin mutanen kuma suna kokawar daukar buhunan abincin, da ake zargin za a kai kasar Jamhuriyar Nijar ne.
- Kotu ta sa a yi wa Murja gwajin kwakwalwa
- Kamfanonin siminti za su rage farashinsa a Najeriya
- Najeriya A Yau: Yadda Za A Ceto Najeriya Daga Mawuyacin Hali
Amma a sanarwar kamfanin da ke tabbatar da aukuwar lamarin, kamfanin na Dangote ya musanta cewa Nijar zai kai kayan abincin.
A shekarar da ta gabata ne Najeriya ta rufe iyakarta da Nijar sakamakon hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum da sojojin kasar suka yi.