Yunwa na kashe yara a asibitocin Gaza — WHO
Yakin da Isra’ila ke yi a Gaza ya kashe aƙalla mutane 31,112, galibi yara da mata.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta ce, wani ayarin agaji da ya kai ziyara a wasu asibitoci biyu a Arewacin Gaza, ya gano munanan yanayi kan yadda yara ke mutuwa saboda yunwa, sakamakon matsanancin karancin abinci, man fetur da magunguna, kamar yadda kafar yada labarai ta TRT ta kasar Turkiyya ta wallafa.
A binciken da kafar ta yi kan abubuwan da aka gano sun kasance, munana.
Shugaban Hukumar WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, “Halin da ake ciki a Al Awda ya kasance mai ban tsoro, saboda daya daga cikin gine-ginen ya lalace”.
- Ɓangaren Lafiya Na Cikin Mummunan Yanayi A Gwamnatin Tinubu — Likitoci
- Ramadan: Hisbah ta kama marasa Azumi 12 a Kano
Ya bayyana haka ne a kafar sada zumunta ta X.
Asibitin Kamal Adwan, wanda shi ne kadai asibitin kula da yara a Arewacin Gaza, ya cika da majinyata.
“Rashin abinci ya yi sanadiyar mutuwar yara 10,” in ji Tedros.
A halin da ake ciki, wata kungiya da ke birnin Geneva, Euro-Med Human Rights Monitor, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar da wata shaida mai tayar da hankali da ke nuna cewa tankunan yakin Isra’ila na kai farmaki a kan Falasdinawa fararen hula da gangan.
Ta ce tankokin Isra’ila sun yi barin wuta kan Falasdinawa fararen hula a ranar Lahadin makon jiya.
Kungiyar da ke da hedkwata a birnin Geneba ta bayyana wadannan laifuffuka a ranar Litinin a matsayin wani bangare na kisan gillar da Isra’ila ke yi wa Falasdinawa a Zirin Gaza.
Euro-Med ta ba da rahoton kararraki da dama kan yadda ake zargin sojojin Isra’ila da su yi wa fararen hula Falasdinawa lugudan wuta da ransu, ciki har da wani mutum a ranar 29 ga Fabrairu da wasu iyalai a ranar 23 ga Janairu, sai wasu mutanen da suka yi gudun hijira a watan Disamban 2023, da wasu iyalai a ranar 20 ga Fabrairu.
Kungiyar ta yi kira a kafa “Kwamitin bincike na kasa da kasa mai zaman kansa wanda ya kware a ci gaba da harin soji da Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza.”
Isra’ila ta ci gaba da kai kazaman hare-hare a Zirin Gaza, bayan kutsawar da Kungiyar Hamas ta yi a kan iyakokin kasar a ranar 7 ga Oktoba, 2023.
Yakin da Isra’ila ke yi a kan Falasɗinawa da ke Gaza – wanda ke cikin kwanaki na 158 – ya kashe aƙalla mutane 31,112, galibi yara da mata, tare da jikkata 72,760, tare da barnata gidajen jama’a da haifar da karancin kayan masarufi.