Yunwa ta sa killatattun zakuna 30 cin naman junansu
Kimanin zakuna dubu 12 ne ake tsare da su a Afirka ta Kudu.
Wasu zakuna 30 da aka killace su aka bar su a cikin yunwa bayan sun samu raunuka lokacin da wani ya kai masu farmaki a matsuguninsu a Afirka ta Kudu, sun rika cin junansu.
An dai bar dabbobin babu abinci na wani lokaci kafin gobara ta cinye harabar da suke a Lardin Free State a Afirka ta Kudu a watan Agustan bana.
- DSS ta gano sabuwar dabarar fashi da makami a Kano
- COVID-19: Buhari ya bukaci daidaito wajen raba rigakafi a duniya
An kashe zaki guda, inda zakuna uku ’yan uwansa suka cinye shi, wasu kuma sun galabaita da yunwa, inda da yawansu suka kasa tsayuwa da kafafunsu, sannan wasu jini yana zuba daga raunukan da suka samu a sakamakon kuna.
Jami’an kula da walwala ne suka gano babbar cibiyar kiwon namun dajin, inda aka ajiye jimillar zakuna da damisa 59, kuma sun ce wannan na daya daga cikin miyagun laifuffukan da suka taba gani a kan dabbobi.
Sufeton Hukumar Kula da Dabbobi (SPCA), Mista Reinet Meyer ya ce: “Abin da muka samu ya girgiza mu.
“Zakuna uku, wadanda su ne sarakunan dawa a daya daga cikin sansanin dabbobin, ba su iya tsayawa ko kadan.
“Da sun yi yunkurin tashi, sai kawai su fadi kasa.
“Mun tuntubi mai gidan don jin ko ya samu wata barna a gonarsa da dabbobin suka yi.
“Ya ce, a’a, babu wani abu da suka lalata,” Meyer ya bayyana wa kafar labarai ta Times Live.
Kimanin zakuna dubu 12 ne ake tsare da su a Afirka ta Kudu.
Sau da yawa ana raba ’ya’ya da iyayensu a lokacin haihuwa domin masu yawon bude-ido su iya ciyar da dabbobin ta hanyar samun kudin shiga.
Ana kiwon kananan zakuna da damisa da yawa a cibiyar, kuma mafarauta suna biyan dubban kudade don kashe jinsin zababbun nau’o’in dabbobi tare da taimakon jami’an yankuna.
Sannan ana sayar da kasusuwansu a kasuwannin Asiya inda ake amfani da su wajen yin magunguna da kayan kwalliya.
Ana samun rahotannin cin zarafin dabbobi a-kai-a-kai, duk da haka ba kasafai ake yanke hukunci a kan masu yin haka ba