Yunwa ta tilasta ’yan Boko Haram 76 mika wuya ga sojoji

Kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 76 ne suka mika wuya ga sojoji bayan da yunwa ta tilasta su yin saranda. Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press (AP) ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa, ‘’yan Boko Haram din wadanda suka galabaita sun rika rokon a ba su abinci a lokacinnda suka mika wuya kamar yadda majiyoyin […]

Yunwa ta tilasta ’yan Boko Haram 76 mika wuya ga sojoji
Yunwa ta tilasta ’yan Boko Haram 76 mika wuya ga sojoji

Kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 76 ne suka mika wuya ga sojoji bayan da yunwa ta tilasta su yin saranda.
Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press (AP) ya ruwaito a shekaranjiya Laraba cewa, ‘’yan Boko Haram din wadanda suka galabaita sun rika rokon a ba su abinci a lokacinnda suka mika wuya kamar yadda majiyoyin soja da na Sibiliyan JTF suka tabbatar masa.
Mutum 76 ciki hard a yara da mata suka mika wuya ga sojoji a ranar Asabar a garin Gwoza mai nisan kilomita 100 (mil 60) Kudu maso Gabas da birnin Maiduguri kamar yadda wani babban soja ya fadi.
An tsare su a hedkwatar soji da ke Maiduguri mahaifar Boko Haram kuma cibiyar yaki da Boko Haram a yanzu inji jami’in wanda ya nanata cewab kada a ambaci sunansa saboda ba a ba shi izinin ya yi Magana da manema labarai ba.
Wadanda aka tsaren sun ce mayakan Boko Haram da dama suna son mika wuya, wani dan Sibiliyan JTF da ya raka su zuwa Maiduguri ya shaida wa Associated Press.
karancin abinci ga mayakan Boko Haram din yana nuni da cewa sojojin Najeriya suna samun nasara wajen dakile hanyoyin da ’yan ta’adda na Boko Haram suke samun kayayyaki a kan iyakokin Najeriya.
Boko Haram dai ta shafe shekara shida tana tayar da kayar baya inda ta hallaka fiye da mutum dubu 20 tare da raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallinsu.
A shekarar 2014 an bayyana Boko Haram da zama kungiyar da ta fi barna da aikata rashin imani a duniya.
An bayar da rahoton cewa sojojin Najeriya suna bayyana cewa daruruwan mayakan Boko Haram sun mika wuya a watan Satumba da Oktoban bara. Kuma sojojin sun yi alkawarin duk wanda ya mika wuya a kashin kansa za a yi kokarin fahimtar da su ta hanyar raba su da guluwi a harkokinsu.
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawari a wata 10 da suka gabata cewa zai kawo karshen Boko Haram, inda ya sauya shugabannin sojojin kasar nan tare da mayar da hedkwatar yaki da Boko Haram zuwa Maiduguri maimakon Abuja.
Sojojin sun rika fatattakar mayakan Boko Haram daga garuruwa da kauyukan da suka ayyana kafa daular Musulunci, sai dai kuma ’yan Boko Haramdin sun koma yakin sari-ka-noke ta hare-haren bam din kunar bakin wake.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya