Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An kammala kaɗa ƙuri’a a wasu yankunan Kano

Akwai rumfar zaɓen da har kawo yanzu kayayyakin zaɓen ba su iso ba.

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An kammala kaɗa ƙuri’a a wasu yankunan Kano

An rufe wasu rumfunan zaɓe bayan kammala kaɗa ƙuri’a a zaɓen ƙananan hukumomin da ke gudana yau Asabar a Jihar Kano.

Daga cikin yankunan da aka kammala kaɗa ƙuri’ar har da Firamaren Gandun Albasa inda akwai aƙalla rumfunan zaɓe 22.

Aminiya ta lura cewa sauran rumfunan zaɓen da ba a kammala kaɗa ƙuri’ar ba akwatunan zaɓe kaɗan ne ba a rufe ba.

Kazalika, wakilinmu ya lura cewa jama’a sun ƙaurace wa zaɓen a wasu rumfunan zaɓen da ke ƙananan hukumomin Tarauni da Nassarawa.

Haka kuma, akwai wata rumfar zaɓe a Ƙaramar Hukumar Nassarawa da har zuwa haɗa wannan rahoton ba a kawo kayayyakin zaɓen ba.