Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An samu jinkirin raba kayan zaɓe a Kaduna 

Lamarin ya sanya masu kaɗa ƙuri’a zaman jiran zuwan kayan zaɓen saɓanin lokacin da aka tsara.

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An samu jinkirin raba kayan zaɓe a Kaduna 

Rijistar Masu Zabe

Jinkirin isar kayan zaɓe da ma’aikata ya haifar da tsaiko a zaɓen ƙananan hukumomin Jihar Kaduna da ke gudana a ranar Asabar.

An shirya fara zaɓen ne da misalin ƙarfe 8 na safe, amma har bayan ƙarfe 10 na safe, ba a fara kaɗa ƙuri’a ba a mafi yawan rumfunan zabe.

Wakilinmu da ya ziyarci wurare da dama a  unguwannin Tudun Wada Badiko da Magajin Gari da Unguwar Sarki, inda ya lura cewa ba a kai kayan zaɓe zuwa rumfunan zaɓe ba.

An tsara fara yin rijista da kaɗa kuri’a da misalin ƙarfe 8:30 na safe kuma a kammala da ƙarfe 2 na rana.

Tsohon Kansila na Unguwar Sarki, Zubairu Shan’una, ya ce, “Har yanzu muna nan muna jiran kayan zaɓe su iso.

“Kamar yadda ka sani, zaɓen ya kamata ya fara da ƙarfe 8:30 na safe, amma har ƙarfe 10 na safe kayan zaɓe ba su iso Unguwar Sarki ba,” in ji shi.

Malam Idris, wakilin jam’iyya a rumfar zaɓe ta Makarantar Sakandare ta Maimuna Gwarzo da ke Tudun Wada, ya ce ya isa wajen zaɓen da misalin ƙarfe 6:30 na safe.

Amma a cewarsa ma’aikatan zaɓen ba su isa wajen ba, kuma ba a raba kayan zaɓe ba.

A Magajin Gari, an samu rikici yayin da wakilan jam’iyyu suka yi ƙorafin samun jinkirin rabon kayan zaɓe.