Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An sanya dokar taƙaita zirga-zirga a Kano
Gwamnatin Kano ta nanata ƙudirin gudanar da sahihin zaɓe na gaskiya da adalci.
Gwamnatin Kano ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta tsawon sa’o’i 18 daga ƙarfe 12:00 na daren yau Juma’a zuwa 6:00 na yammacin gobe Asabar.
Aminiya ta ruwaito cewa gwamnatin ta ayyana dokar ce bayan tuntuɓar hukumomin tsaro kamar yadda wata sanarwa da Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin Gida, Baba Halilu Dantiye ya fitar a yammacin wannan Juma’ar.
- A kamo min Bello Turji — Ministan Tsaro
- Yadda rashin wutar lantarki ya zame min alheri — Mai cajin waya
Baba Dantiye ya buƙaci jama’a da su mutunta wannan doka ta taƙaita zirga-zirga domin bayar da haɗin kai wajen tabbatar da an gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar cikin aminci.
Kwamishinan ya nanata ƙudirin gwamnatin na tabbatar da an gudanar da tsarkakken zaɓe na gaskiya da adalci.
Sanarwar da Kwamishinan ya fitar ta ƙara da cewa, dokar ta shafi dukkan ƙananan hukumomin jihar 44 da gundumomin zaɓe 484 da ke faɗin jihar.
Sanya dokar dai na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 gabanin zaɓen ƙananan hukumomin Kano da zai gudana a gobe Asabar, 26 ga watan Oktoba.