Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Ba ni da shirin yi wa APC zagon ƙasa — Baloni

Ya ce bai taɓa zuwa wajen wani ɗan siyasa da nufin taimaka masa domin samun kujerar takara.

Zaɓen Ƙananan Hukumomi: Ba ni da shirin yi wa APC zagon ƙasa — Baloni

Shugaban Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, Muktar Baloni, ya ƙaryata zargin da ake yi masa na cewar zai yi wa jam’iyyar APC zagon ƙasa, saboda rasa kujerar takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe. 

Baloni, ya ce ko kaɗan ba shi da niyyar butulce wa APC kuma ba shi da wata mummunar niyya ga ɗan takararta.

Shugaban, wanda wa’adin mulkinsa na shekara uku zai ƙare a watan Nuwamba, jam’iyyar APC ta ƙi sake ba shi takara a zaɓen da ke tafe.

Sai dai duk da haka ya buƙaci ’yan jam’iyyar da su tashi tsaye wajen neman ƙuri’ar mutane domin kai jami’yyar ga matakin nasara.

Baloni, ya bayyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki da shugabanin jam’iyyar a mazaɓarsa ta Kabala da suka shirya.

An shirya taron ne tare da ƙaddamar da littafi mai ɗauke da ayyukan da ya ya yi cikin shekara uku a mulkinsa.

“Maganar yin zagon ƙasa duk ba shi ba ne. Ita harkar nan ta siyasa idan ka ci zaɓe ana cewa ka ci zaɓe ne. Akasin haka kuma kai ake cewa ba ka yi nasara ba. Ba a cewa wani ne ya sa ka ci ko ka faɗi zaɓe.

“A matsayinmu na Muslim masu tawakkali da imani, ya kamata mu sani cewa mulki ko wakilci daga Allah ne kuma Allah ke ba da shi ga wanda ya so ta yadda ya so a lokacin da ya so.

“Babu wanda ya isa ya ba ka ko ya hana ka. Muna bayar da gudunmuwar da zamu iya bayarwa, sauran kuma ya rage ga masu takara su fita su je neman yardar al’umma,” in ji shi.

Ya kuma ƙaryata zancen da ake yi na cewa ya nemi ya sake tsayawa takara, amma jam’iyyarsa ta ƙi amincewa da buƙatarsa.

Ya ce shi bai taɓa neman wani ya taimake shi a tsayar da shi takara ba bayan kammala wa’adinsa.

“Na zauna da shugabanin jam’iyya a matakin ƙaramar hukuma, inda na shaida musu ba na neman sake tsayawa takara saboda hurumi ne na manyan a jam’iyya su ce ga ɗan takarar da za a bi.

“Saboda haka ni ban je wajen wani babban ɗan siyasa na faɗa masa cewa ina buƙatar sake yin takara ba,” in ji shi.

A jawabinsa shugaban jam’iyyar APC a mazaɓar Kabala, Abdullahi Abubakar, ya bayyana cewa ba a taɓa samun shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa da ya yi aiki kamar Baloni ba.

Ya ce hakan ne ya sa suka buga littafi domin ajiyewa tare da bai wa duk wani shugaban ƙaramar hukumar don ganin irin ayyukan da ya yi.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025